Ayyukan Femi Gbajabiamila 8 A Matsayinsa Na Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tinubu

Ayyukan Femi Gbajabiamila 8 A Matsayinsa Na Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tinubu

  • Femi Gbajabiamila, tsohon kakakin Majalisar Wakilai ta ƙasa ya ajiye muƙaminsa domin zama shugaban ma'aikatan gwamnatin Tinubu
  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da naɗin Gbajabiamila matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa a ranar 2 ga watan Yuni
  • Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ne ya ƙirƙiri ofishin shugaban ma'aikatan a shekarar 1999 domin bin irin salon gwamnatin ƙasar Amurka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Tsohon kakakin Majalisar Wakilai ta tara, Femi Gbajabiamila ya ajiye muƙaminsa daga majalisar domin karɓar muƙamin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa da Bola Tinubu ya ba shi.

A ranar 2 ga watan Yunin shekarar 2023 da muke ciki ne, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da naɗin Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma'aikatan.

A shekarar 1999, a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo na farar hula ne aka ƙirƙiro ofishin, domin koyi da irin salon mulkin ƙasar Amurka.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Mayar Da Wasu Hukumomi 2 a Karkashin Ofishin Kashim Shettima

Ayyukan ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa 8 da ya kamata ku sani
Ayyuka 8 da Gbajabiamila zai gudanar a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Tinubu. Hoto: Femi Gbajabiamila, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Menene takamaiman aikin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa?

Kamar yadda jaridar This Day ta wallafa, tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya yi bayani kan ayyukan ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasar, kamar yadda yake a ƙasar Amurka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A dalilin haka, ayyukan shugaban ma'aikatan na yanzu ba za su bambanta da ayyukan shugabannin ma'aikatan fadar gwamnatin na baya ba.

A saboda haka mun tattaro muku ayyukan da Femi Gbajabiamila zai fuskanta a sabon ofishin da ya samu a yanzu.

Jerin ayyukan ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa

1. Shiryawa shugaban ƙasa zama da mutane

2. Kyautata Alaƙa tsakanin shugaban ƙasa da sauran ɓangarori na gwamnati

3. Shi ne zai sada ministoci da shugaban ƙasa

4. Shi ne zai jagoranci dukkanin ma'aikatan fadar shugaban ƙasa

5. Shi ne kuma zai riƙa bai wa shugaban ƙasa shawara kan dukkan al'amuran ƙasa

Kara karanta wannan

Daga Rantsar Da Shi Sabon IGP Ya Aike Da Muhimmin Gargadi Ga Miyagu Da Makiyan Najeriya

6. Shi ne kuma zai riƙa sanya idanu akan ma'aikatan fadar shugaban ƙasa

7. Zai kuma riƙa kula da shige da ficen al'umma a ofishin shugaban ƙasa

8. Haka nan shi ne zai riƙa kula da shige da ficen sakonni a fadar gwamnatin

Tinubu ya naɗa Gbajabiamila a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa

A baya Legit.ng ta kawo muku rahoto kan sanarwar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar, ta naɗin tsohon kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa.

Haka nan kuma shugaban ya sanar da naɗin tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa.

Tuni tsohon shugaban ma'aikatan na lokacin Buhari, Ibrahim Gambari ya miƙawa sabon shugaban ragamar tafiyar da ofishin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng