Shugabannin PDP 7 da Suka Yi Murabus, Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC
- Tsoffin shugabannin PDP 7 a jihar Imo sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki ranar Litinin, 19 ga watan Yuni
- Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ne ya karɓe su hannu bibbiyu a fadar gwamnatinsa da ke Owerri
- Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan sun yi murabus daga muƙamansu kuma sun fice daga PDP
Imo State - Mambobi 7 na kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP reshen jihar Imo (SWC), waɗanda suka fice daga jam'iyyar a 'yan kwanakin da suka wuce, sun shiga jam'iyyar APC.
The Cable ta tattaro cewa shugabannin PDP 7 a matakin jiha da suka ɗauki wannan mataki sun ƙunshi, mataimakin shugaba, Martin Ejiogu, da kakakin PDP na jiha, Collins Opuruozor.
Sauran sun haɗa da Sakatare, Greg Nwadike, shugaban matasan PDP, Greg Nwadike, shugabar mata, Maria Mbakwe, ma'ajiyin kuɗi, Josiah Eze, da mataimakin shugaban PDP na shiyyar Orlu, Chibuisi Obido.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa dukkan waɗannan shugabannin PDP a matakin jihar Imo, sun yi murabus a kwanakin baya, daga bisani suka sauya sheka zuwa APC ranar Litinin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Abinda ya sa PDP ta wayi gari cikin rigingimu - Tsohon kakaki
A ranar Lahadin da ta gabata, tsohon mai magana da yawun PDP, Mista Opuruozor, ya yi zargin cewa Sakataren jam'iyya na kasa, Samuel Anyanwu, ne ya haddasa duk abinda ke faruwa.
A cewarsa, Anyanwu, tsohon sanatan da ya zama Sakataren PDP na ƙasa, ya riƙa amfani da karfin ikonsa yana yaƙar mambobin kwamitin gudanarwa na jihar Imo.
Daily Post ta rahoto a kalamansa yana cewa:
"Tunda Sanata Anyanwu ya zama Sakataren PDP ta ƙasa ya fara yaƙar mambobin kwamitin gudanarwa na jiha ba ɗaga kafa, har mambobin da ba ruwansu bai bari ba, haka ya riƙa musu barazana."
Yadda gwamna Uzodinma ya karɓi masu sauya shekar hannu biyu
Rahoto ya nuna cewa a ranar Litini, Gwamna Hope Uzodinma, ya tarbi tsaffin shugabannin PDP da suka koma APC a fadar gwamnatinsa da ke Owerri, babban birnin Imo.
Duk da babu cikakken bayani kan abinda aka tattauta a taron amma an ce tsoffin jiga-jigan PDP sun yi mubaya'a tare da tabbatar da goyon bayansu ga Uzodinma.
Gwamna Uzodinma na jam'iyyar APC na kokarin tazarce kan kujerarsa a zaben gwamnan Imo da ke tafe a watan Nuwamba.
Gwamna Aliyu Ya Yi Badda Kama, Ya Shiga Keke Napep Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibiti
A wani rahoton na daban kuma Gwamnan Sakkwato ya yi badda kama, ya kai ziyarar ba zata babban Asibiti na musamman a cikin birni.
Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya kai ziyarar ba zata babban Asibiti na musamman a cikin garin Sokoto domin gane wa idonsa yadda ake duba marasa lafiya.
Gudaji Kazaure Ya Lissafa Jerin Sunayen Ministoci Da Muƙarraban Buhari Da Ya Kamata Tinubu Ya Kama Su Da Dalilai, Bidiyon Ya Yadu
Asali: Legit.ng