Kujerar Minista Na Tangal-Tangal – An Zuga Tinubu Ya Watsar da Tsofaffin Gwamnoni

Kujerar Minista Na Tangal-Tangal – An Zuga Tinubu Ya Watsar da Tsofaffin Gwamnoni

  • Kungiyar Northern Progressives Union ta na so a tuna sakamakon zaben 2023 wajen nadin mukamai
  • Shugaban NPU, Mohammed Ibrahim Kiyawa ya ba Bola Tinubu shawarar wadanda zai tafi da su
  • Jam’iyyar PDP ta doke APC a wasu Jihohin Arewa, Kiyawa su na ganin laifin Gwamnonin lokacin ne

Abuja - Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC daga Arewacin Najeriya sun gabatar da bukatarsu zuwa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Vanguard ta ce shugaban ‘yan kungiyar NPU ta masu sha’awar cigaba a yankin Arewacin Najeriya sun ce ka da a ba wasu tsofaffin Gwamnoni mukamai.

Shugaban NPU, Mohammed Ibrahim Kiyawa ya fitar da jawabi, ya ce akwai tsofaffin gwamnoni da ba za su iya tabuka komai a gwamnatin Bola Tinubu ba.

Tinubu
Bola Tinubu wajen kamfe a Bauchi Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Mohammed Ibrahim Kiyawa yake cewa bai ga dalilin dauko wadanda su ka gagara abin kirki a lokacin da su ke Gwamnoni ba, kuma a ba su mukamai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Dauko Batun Karin Albashi, An Kafa Kwamitoci Na Musamman

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jawabin Mohammed Ibrahim Kiyawa

"Shugabanni ne da ba su dace da halin da ake ciki a yau da kuma manufar gwamnatin nan mai-ci na tsarin ‘Renewed Hope’ ba.
Mu ne ‘yan a-mutun APC a bangaren kasar nan, saboda haka mu ke kira ga shugaban kasa da APC ayi watsi da maganar kawo sunayen tsofaffin Gwamnoin yankin wajen samun mukaman da za a bada, domin ba su cancanta ba.

- Mohammed Ibrahim Kiyawa

Zargin da ake yi wa tsofaffin Gwamnonin

Kiyawa ya ce wasu tsofaffin Gwamnonin jihohin sun taimakawa ‘yan adawa ne a zaben 2023, wasunsu kuma su ka boye kudi yakin neman zabe.

The Cable ta rahoto NPU ta ce a lokacin da Bola Tinubu ya ke fafutukar zama shugaban kasa, 'yan siyasar ba su iya ba APC nasara a jihohinsu ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Tsige Duk Masu Kula da Hukumomi, Cibiyoyi da Kamfanonin Gwamnati

Ana zargin kungiyar ta na magana ne a kan su Mohammed Badaru wanda su ka ce ya rike kudin kamfe, hakan ya jawo PDP tayi nasara a wasu garuruwa.

Kiyawa ya jero laifuffukan ‘yan siyasar da cewa ba su yi kokari a ofis ba, kuma zamanin da ake ciki ya wuce da yayinsu, har ta kai a ba su mukamai.

Kiyawa ya na ganin babu jihohin Arewa da su ka taimakawa APC kamar Jigawa, Yobe da Zamfara

Za a kara albashin ma'aikata?

A rahoton da mu ka samu dazu, an fahimci Gwamnatin Bola Tinubu za ta duba bukatun da Shugabannin kungiyoyin NLC da TUC su ka gabatar mata.

‘Yan kwadago su na so a tanadi motocin haya masu aiki da gas kuma ayi wa ma’aikata karin albashi a sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng