Jigon NNPP A Legas Ya Ba INEC Muhimmiman Shawarwari 2 Dangane Da Zabukan Kogi, Imo da Bayelsa Da Ke Karatowa

Jigon NNPP A Legas Ya Ba INEC Muhimmiman Shawarwari 2 Dangane Da Zabukan Kogi, Imo da Bayelsa Da Ke Karatowa

  • Wani jigo a jam’iyyar NNPP, Adekunle Razaq Aderibigbe, ya aikewa da Hukumar Zaɓe Mai Zaman kanta ta Ƙasa (INEC), da saƙo game da zaɓen da ke tafe a jihohin Imo, Kogi, da Bayelsa
  • Aderibigbe ya ce an tafka abin kunya da dama a zaɓen da ya gabata, ta yadda hatta wasu daga cikin jami’an INEC, ba su iya tantance jam’iyyun dake kan takardar zaɓe ba
  • Aderibigbe, wanda tsohon ɗan takarar majalisar dokokin jihar Legas ne, ya buƙaci hukumar zaɓen ta horar da jami’anta kan yadda za su yi ingantaccen aiki lokacin zaɓe

Ikorodu, Legas – Adekunle Razaq Aderibigbe, jigo a jam’iyyar NNPP a jihar Legas, ya bukaci hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), da ta tabbatar da an yi zaɓen gwamna na gaskiya a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Faɗi Babban Jigon da Alamu Suka Nuna Zai Koma APC, Ya Roƙe Shi Alfarma 1

Da yake zantawa da Legit.ng, Aderibigbe, wanda ya tsaya takarar kujerar ɗan majalisar dokokin jihar Legas a mazaɓar Ikorodu 1 a zaɓen da ya gabata, ya jaddada bukatar nuna ƙwarewa daga ma'aikatan INEC, a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaɓukan cike gurbi.

Jigon NNPP a Legas ya bai wa INEC shawarwari
Jigo a jam'iyyar NNPP reshen jihar Legas ya shawarci INEC kan Zaben Kogi, Imo da Bayelsa. Hoto: Aderibigbe, INEC Nigeria
Asali: Facebook

Jigon na NNPP ya buƙaci INEC ta gudanar da sahihin zaben gwamna a Kogi, Imo, Bayelsa

Aderibigbe ya koka kan yadda aka cire sunan dan takarar jam’iyyar NNPP a takardun kaɗa zaɓe lokacin zaɓen watan Maris da ya gabata. Don haka ya shawarci INEC da ta kara kula wajen gudanar da ayyukanta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A baya INEC ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓukan gwamnonin guda uku a rana ɗaya, wato ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Kara karanta wannan

Yadda Peter Obi Ya Ci Amanar Atiku Abubakar Gabanin Zaben Shugaban Kasa Na 2023, Sabbin Bayanai Sun Fito

A cewar Aderibigbe:

“Domin zaɓe mai gabatowa a jihohin Imo, Kogi da Bayelsa, saƙona zuwa ga INEC shi ne da farko ta kare mutuncinta, kimarta da 'yancin kan da take da shi ta hanyar bugo ƙuri'un zaɓen da za su bai wa dukkan jam’iyyu da ‘yan takara damar a kaɗa musu ƙuri'a.”
“Ba shakka jama'a da dama sun shiga ruɗu a zaɓen da ya gabata, ta yadda wasu ba su yi zaɓe ba, sakamakon kasa tantance jam’iyyar da suke so su zaɓa, saboda an cire sunan jam’iyyar ko na ‘yan takararta, an bar iya tambarin jam’iyya kawai a kan takardun ƙuri'un zaɓen."

Ya ƙara da cewa abin kunya ne da har jami’an INEC da ke aikin gudanar da zaɓuka a rumfunan zaɓen suka kasa tantance jam’iyyu, ballanta kuma masu zaɓe.

Sannan ya yi kira ga INEC da ta horar da jami’anta sosai, sabili da wasu daga cikin malaman zaɓen, sai a rumfunan zaɓe ne aka koyar da su yadda ake yin wasu abubuwan.

Kara karanta wannan

Shin Dagaske EFCC Ta Gayyaci Tsohon Shugaban Kasa Kan Wawure Kuɗi? Gaskiya Ta Bayyana

Abubuwa biyu ya kamata INEC ta yi, a cewar Aderibigbe

Aderibigbe ya shawarci hukumar INEC kan cewa ta tabbatar da ta yi waɗannan abubuwan guda biyu:

1. Ya kamata INEC ta kiyaye mutuncinta da kuma ‘yancin cin gashin kanta.

2. Hukumar ta horar da ma'aikatanta.

Ya kuma bayyana cewa yana sa ran jam'iyyarsa ta NNPP, za ta yi abin a zo a yaba idan INEC ta yi gyare-gyare a harkokin gudanar da zaɓen nata.

Ko Tinubu zai kori shugaban INEC bayan dakatar da Bawa da Emefiele? Lauya ya yi bayani

A wani labarin na daban da Legit.ng ta kawo muku a baya, fitaccen lauyan rajin kare haƙƙin bil'ama, Malcolm Omirhobo, ya bayyana cewa mutane su daina tunanin cewa Tinubu zai dakatar da shugaban INEC, Mahmoud Yakubu.

Ya ce duk masu jiran su ga Tinubu ya dakatar da shi, to lallai suna jiran gawon shanu ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng