Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa Ta Magantu Kan Kalaman Da Mijinta Ya Yi, Ta Ce Kalaman Ba Gaskiya Ba Ne

Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa Ta Magantu Kan Kalaman Da Mijinta Ya Yi, Ta Ce Kalaman Ba Gaskiya Ba Ne

  • Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa ta yi zazzafan martani, dangane da kalaman da mijinta Sanata Adamu Bulkachuwa ya yi a zauren Majalisar Dattawa ta tara
  • Sanata Adamu a yayin zaman ƙarshe na majalisar ta tara, ya yi iƙirarin cewa ya sanya matarsa yi wa wasu daga cikin sanatocin alfarma a shari'o'insu
  • Kalaman nasa sun bar baya da ƙura, inda suka janyo cece kuce musamman a tsakankanin ma'aikatan shari'a da ma wasu daga cikin 'yan ƙasa

Babbar alkaliya Zainab Bulkachuwa, wacce mata ce ga Adamu Bulkachuwa, tsohon sanatan Bauchi ta Arewa a Majalisar Dattawa ta tara, ta yi magana don kare mutuncin aikinta.

Ta na mayar da martani ne dangane da kalaman da mijin nata ya yi na cewa ya yi amfani da damarsa wajen nemawa abokan aikinsa alfarma daga wurinta, a sanda take shugabar kotun daukaka ƙara, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

"Wannan Bata Da Kunya": Hirar Wata Budurwa Da Wani Saurayi Ta Janyo Mahawara a Yanar Gizo

Zainab Bulkachuwa ta musanta kalaman da mijinta ya yi
Mai shari'a Zainab Bulkachuwa ta bayyana cewa kalaman da mijinta ya yi ba haka suke ba. Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

Kalaman da Sanata Adamu Bulkachuwa ya yi

Bulkachuwa a yayin zaman bankwana na zauren Majalisar Dattawa ta 9 ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ina shaida wasu fuskoki a wannan zauren da suka zo wurina suka nemi taimako a lokacin da matata ke shugabar kotun ɗaukaka ƙara, kuma tabbas na yi musu hakan."
"Kuma dole ne in godewa matata, musamman yadda na riƙa shiga cikin haƙƙinta da na aikinta a yayin da take ofis, kuma ta kasance mai aminta da buƙatun da na je da su, wajen taimakon abokan aikina."

Kalaman na Bulkachuwa sun tayar da ƙura, inda Olisa Agbakoba, tsohon shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), ya yi kira ga jami'an tsaro da su kama tsohon sanatan.

Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa ta musanta kalaman na mijinta

Sai dai a wata sanarwa da mai shari’a Zainab Bulkachuwa ta fitar, ta ce batun babu ƙanshin gaskiya ko kadan a cikinsa.

Kara karanta wannan

"Har Lakada Min Duka Ta Taba Yi": Magidanci Ya Garzaya Kotu Neman a Korar Masa Tsohuwar Matarsa Daga Gida

A kalamanta:

"Hankalina ya karkata kan faifan bidiyon abinda mijina Sanata Adamu M. Bulkachuwa ya faɗa."
"Ina so in bayyanawa duniya cewa, ban taɓa karya rantsuwar da na ɗauka ba ta hanyar taimakon wata jam'iyya da ta bayyana a gabana yayin shari'a, a cikin tsawon shekaru 40 da na yi ina hidima ga ƙasata."
"Hukunce-hukunce na a ko yaushe suna kasancewa ne a kan doron gaskiya, doka kuma bisa fahimtata da kuma rantsuwar da na yi ta ofis."
“Haka nan kuma, a lokacin da nake shugabancin kotun ɗaukaka ƙara, abokan aikina a kotun za su iya bayar da shedar cewa, ban taɓa yin katsalanda ga wani daga cikin alƙalan kotun ba, wajen gudanar da ayyukansa na shari’a.”

Tun da farko, a wata hira da gidan rediyon BBC Hausa, Bulkachuwa ya ce an yi wa kalaman nasa mummunar fassara, inda ya ƙara da cewa, tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ne ya datse shi a lokacin da yake bayani.

Kara karanta wannan

"Mutane Ba Su Fahimci Kalamai Na Ba', Sanata Bulkachuwa Ya Fede Komai Kan Zargin Sauya Hukuncin Da Matarsa Alkaliya Ke Yankewa

Babban lauya ya soki Sanata Bulkachuwa bisa kalaman da ya yi

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan babban lauya Jibrin Samuel Okutepa da ya caccaki Sanata Adamu Bulkachuwa bisa kalaman da ya yi a zauren Majalisar Dattawa ta tara.

Lauyan dai ya caccaki Bulkachuwan ne a yayin da yake mayar da martani kan sakin bakin da ya yi a zaman majalisar na ƙarshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng