Kano: Abba Gida-Gida Zai Tona Yadda Matar Ganduje Ta Mallaki Kashi 70 Na Filayen Makarantu

Kano: Abba Gida-Gida Zai Tona Yadda Matar Ganduje Ta Mallaki Kashi 70 Na Filayen Makarantu

  • Abba Kabir Yusuf ya caccaki yadda aka rika cin filayen makarantu a gwamnatin Abdullahi Ganduje
  • Sabon Gwamnan Kano ya sha alwashin karbo wadannan filaye domin su koma hannun talakawa
  • A jawabin da ya yi a jiya, Gwamnan ya ce za su fito da sunayen wadanda aka saidawa wurin karatu

Kano - Mai girma Abba Kabir Yusuf ya yi magana a game da rushe wasu gine-gine da gwamnatinsa ta ke yi, ya bayyana dalilin da ya sa aka kama wannan layi.

Da yake jawabi a garin Kano, Legit.ng Hausa ta samu bidiyon da aka ji Gwamna Abba Kabir Yusuf ya na kokawa a kan yadda aka rika cinye filayen makarantu.

Gwamnan ya zargi gwamnatin Abdullahi Ganduje da shiga cikin makarantu, ta saida filaye, ya ce mai dakin tsohon Gwamna ce ta mallaki mafi yawan filayen.

Kara karanta wannan

An Zabo Mana Bala'i: Kanawa Sun Fusata Da Rushe-Rushen Abba, Sun Hana Rushe Gidajensu

Gwamnan Kano
Sabon Gwamnan Kano, Abba Gida Gida Hoto: Engr Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Da yake jawabi a Africa House a ranar Lahadi, sabon Gwamnan ya sha alwashin fitar da sunayen mutanen da aka yanki filayen makarantu aka saida masu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, wasu daga cikin manyan mutanen da su ka amfana da wannan badakala da aka yi ne su ke fitowa su na suratai domin tunzura mutanen Kano.

Gwamna Abba ya ce da sake!

Abba Yusuf yake cewa a maimakon a gina dakunan karatu da wurin kwanan dalibai, sai gwamnatin da ya gada ta rika amfani da filayen domin gashin kan ta.

Gwamnan ya nuna ba zai bari a cigaba da tafiya a haka ba, zai dawo da duk filayen al’umma.

Makeken fili a makarantar Legal har da dakin karatu a wurin, ya je ya kwace, ya yi fulotai na alfarma a ciki, 70% na goggo ne da ‘ya ‘yanta.

Kara karanta wannan

“Baba Tinubu Lokacinmu Ne Mu Zama Ministan FCT”: Yan Asalin Abuja Sun Koka

Za mu wallafa sunayensu, mu na nan da su. Ai wannan wuri na talakawa ne ko?
Kamata ya yi ita ma makarantar a gina dakuna, a fitar da wuraren wasanni yara, a gina wuraren karatu da wuraren da yara za sus an a makaranta su ke.
Har akwai manyan da su ke surutai, su ma sunayensu ya na ciki, za mu buga idan Allah ya yarda.

- Abba Kabir Yusuf

Gyara gwamnatin Abba za tayi

Kabiru Dakata wanda shi ne shugaban kungiyar CAJA ya ce an yanka filayen makarantu an rabawa shafaffu da mai, su kuma su ka saidawa jama’a.

Kamar yadda yake bayani a ranar Lahadi, Dakata ya ce Abba Kabir Yusuf gyara ya zo yi, kuma shi yake yi, ya na mai fatan Allah kuma zai taimakeshi shi.

Harkar ilmi a Kano

An fitar da sanarwa cewa masu neman yin digirgir a kasashen ketare za su iya neman gurbin karatu a shafin www.kanostategov.ng./scholarship.

An ji labari Gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta zakulo yaran da za a kai karatu zuwa kasashen waje. Sakataren gwamnatin jihar Kano ya sanar da haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng