“Aiki Ne Ya Tara Mu a Nan Ba Wasa Ba”: Alkalin Kotun Zabe Ga Melaye
- Wakilin tattara sakamakon zabe na jam'iyyar PDP na kasa, Dino Melaye, ya halarci zaman kotun zaben shugaban kasa da ke zama a Abuja
- Melaye ya yi ikirarin cewa an tafka daidai ba a jihohin Sokoto, Benue, Borno da Lagas yayin zaben shugaban kasa
- Dan takarar gwamnan na PDP a jihar Kogi ya ce ya samu bayanai daga wakilan jam'iyyarsa a wadannan jihohi da ya ambata
FCT, Abuja - Babban alkalin kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa, Haruna Tsammani, ya fada ma dan takarar gwamna na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kogi, Dino Melaye, da ya amsa tambayoyin da aka yi masa domin dai kotun zaben ba wajen wasa bane.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Justis Tsammani ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 16 ga watan Yuni, a Abuja yayin da lauyan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Afolabi Fashanu (SAN) ke yi wa Melaye tambayoyi.
An tattaro cewa Melaye ya shafe mafi yawan lokaci yana karkatar da tambayoyi, lamarin da ya sa mambobin kotun gaggauta shiga lamarin.
Justis Tsammani ya bukaci lauyan masu kara, Chris Uche (SAN) da ya sa Melaye ya amsa tambayoyin da aka yi masa, yana mai cewa: "Aiki ne ya tara mu a nan ba wasa ba."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da farko Melaye ya fada ma kotun cewa an tafka kuar-kurai a jihohin Sokoto, Benue, Borno da Lagas yayin zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Ya ce ya yi ikirarin ne bisa ga bayanan da ya samu daga wakilan PDP da ke wajen.
Melaye wanda ya kasance wakilin tattara sakamako na PDP na kasa ya ce ya kasance a wajen da taimakon fasa saboda wasu wakilan jam'iyyar sun aike masa da bidiyoyi kai tsaye.
Ya yi ikirarin cewa wakilan PDPn basu sanya hannu a sakamakon zabe ba saboda zargin zamba da sauran magudi da aka tafka.
Jigon na PDP ya kuma ce wadannan dalili na sama yasa ya bar cibiyar tattara sakamako na kasa kafin a kammala shirin.
Ka halarci zaman kotun zabe don marawa Atiku baya: Melaye ga Makinde
A wani labarin, Legit.ng ta rahoto a baya cewa dan takarar gwamnan PDP a zaben jihar Kogi mai zuwa, Dino Melaye, ya baiwa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo sharadi guda da zai tabbatar da yunkurinsa na yin sulhu da Atiku Abubakar.
Da yake martani ga ikirarin Makinde na cewar PDP ta fara farfadowa, Melaye ya bukaci gwamnan ya halarci zaman kotun zaben shugaban kasa na 2023 don nuna goyon baya ga Atiku da PDP.
Asali: Legit.ng