'Lawan Bai Bari Na Gama Fadan Abin Da Ke Zuciyata Ba', Bulkachuwa Ya Yi Karin Haske Kan Batun Matarsa Alkaliya
- Tsohon sanatan Bauchi ta Arewa, Adamu Bulkachuwa ya musanta cewa yana da tasiri wurin hukuncin da matarsa ke yankewa.
- Sanatan ya bayyana haka ne a wata hirarsa da BBC Hausa, inda ya ce mutane da dama basu fahimci kalamansa ba
- Kalaman da Sanata Bulkachuwa ya yi a lokacin zaman majalisar dattawa ta tara kuma na karshe ya jawo kace nace a tsakanin mutane
FCT, Abuja - Tsohon sanatan Bauchi ta Arewa a majalisa ta tara, Adamu Bulkachuwa ya musanta cewa yana da tasiri wurin hukuncin da matarsa ke yankewa a kotu.
Sanatan wanda shi ne mijin Zainab Bulkachuwa, tsohuwar shugabar kotun daukaka kara ta Tarayya, ya ce Ahmed Lawan ya yanke masa magana.
Sanatan ya na kokarin godewa matarsa ne akan taimakon da take bayarwa
Bulkachuwa a zaman karshe na majalisar dattawa ta tara ya ce yana neman taimako wa abokansa a wurin matarsa kafin Ahmed Lawan ka katse shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daily Trust ta ce lokacin zaman majalisar na karshe, Bulkachuwa yace:
"Ina ganin fuskoki a wannan majalisa da suka zo wurina neman taimakon matata lokacin tana shugabar kotun daukaka kara, ina da tabbacin...
"Ina mika godiya musamman ga matata wacce ta taimaka min sosai a lokacin da take kotun daukaka kara da kuma abokai na."
Da yake hira da BBC Hausa, Bulkachuwa yace ba a fahimci kalamansa ba, ya ce tsohon shugaban majalisar, Ahmed Lawan shi ya katse shi yana cikin bayani, cewar Premium Times
Sanatan ya ce Ahmad Lawan ya katse shi ba tare da barinsa ya karisa bayani ba
A cewarsa:
"Gaskiya ba a ma bar ni na gama ba, ina cikin gode mata da cewa ta taimakeni a matsayinta na lauya ni kuma dan siyasa.
"Na so na kara bayanai sosai akan irin taimakon da ta bayar kamar yadda sauran kwararru su ke bayarwa a matakansu.
"Ku sani wannan taimako bai shafi wata hanyar da ba ta dace ba.
"A zamana da ita ban taba sauya mata ra'ayi akan wani hukunci na ofishinta ba, irin wadannan ba ma maganarsu a gida."
Babban Lauya Ya Caccaki Sanata Adamu Bulkachuwa Kan Subut Da Baka Da Ya Yi
A wani labarin, wani babban lauya ya koka kan yadda manyan kasar nan basa bin doka.
Lauyan, Jibrin Samuel ya ce kalaman tsohon sanatan Bauchi, Adamu Bulkachuwa ya nuna rashin bin doka na manyan kasar.
Sanatan ya yi tuntuben harshe inda ya ce yana tsoma baki cikin hukuncin da matarsa ke yankewa a kotu.
Asali: Legit.ng