Yawan Kwanakin Da Obasanjo, Yar’adua, Da Sauransu Suka Dauka Kafin Nada Ministocinsu
- Bayanai sun bayyana game da adadin kwanakin da tsoffin shugabannin kasa tun daga kan Obasanjo zuwa Buhari suka dauka kafin su nada ministoci
- Rahoton ya nuna cewa Buhari ne ya shafe kwanaki mafi yawa kafin ya nada yan majalisarsa
- Obasanjo ya nada ministocinsa cikin mako guda bayan rantsar da shi a zangonsa mulkinsa na farko
Bayyana sun bayyana game da tsawon lokacin da ya dauki tsoffin shugabannin Najeriya, Olusegun Obasanjo, Umaru Musa Yar’adua, Goodluck Jonathan, da Muhammadu Buhari kafin su nada ministocinsu bayan rantsar da su.
Kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto, ya dauki Obasanjo tsawon kwanaki 5 kafin ya kafa majalisarsa lokacin da ya nada ministocinsa a ranar 4 ga watan Yuni
A zangonsa na biyu, Obasanjo ya shafe kwanaki 25 kafin ya nada ministocinsa a ranar 23 ga watan Yunin 2003.
Marigayi Yar'adua, wanda ya karbi mulki a hannun Obasanjo, ya tsaya har zuwa ranar 27 ga watan Yulin 2007, wanda ya yi daidai da kwanaki 59 bayan hawansa kujerar shugabanci.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A nasa bangaren, Jonathan ya shafe kwanaki 30 kafin ya nada ministocinsa a ranar 28 ga watan Yunin 2011 bayan an rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2011.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya fi kowa dadewa kafin ya kafa majalisarsa tun bayan dawowar damokradiyya a 1999, domin dai ya jira har ranar 30 ga watan Satumba kafin ya sanar da ministocinsa bayan ya karbi mulki a 2015.
Buhari ya dan gyara a zangonsa na biyu inda ya sanar da nadin ministocinsa kwanaki 54 bayan rantsar da shi a ranar 22 ga watan Yulin 2019.
Abun tambaya a yanzu shine har tsawon wani lokaci zai dauki shugaban kasa Bola Tinubu kafin ya sanar da ministocinsa.
Ku tuna cewa majalisar dokokin tarayya ta aiwatar da wani kudiri inda ya wajabta sanar da ministoci cikin kwanaki 60 bayan shugaban kasa ya kama aiki.
Shugaban kasa Tinubu ya nada ministoci 27? gaskiya ta bayyana
Legit.ng ta rahoto a baya cewa an gano cewa jerin sunayen sabbin nade-nade 27 da wasu sabbin ma'aikatu da ake zargin shugaban kasa Bola Tinubu ya samar kuma suka karade Facebook na bogi ne.
Kamar yadda Africa Check, wani dandamalin binciken kwakwaf ya rahoto, ana ta yada jerin sunayen mutanen 27 wanda aka tabbatar da karya ne, a shafukan Facebook, tare da ikirarin cewa shugaban kasa Tinubu ya soke wasu kujerun ministoci.
Asali: Legit.ng