Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Fitar da Jerin Sunayen Hadimai da Mukarabansa

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Fitar da Jerin Sunayen Hadimai da Mukarabansa

  • Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi nadin mukamai
  • An maido Sani Abdulkadir Dambo domin ya rike hukumar tattara haraji ta jihar Kano watau KIRS
  • Gwamnan jihar Kano ya amince da nadin masu bada shawarwari da masu taimaka masa

Kano - A wata sanarwa da ta fito daga shafin Sakataren yada labaran Gwamnan jihar Kano, an nada sabon shugaban hukumar haraji watau KIRS.

Mai girma Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Alhaji Sani Abdulkadir Dambo a matsayin sabon shugaban da zai jagoranci hukumar KIRS ta jihar.

Kafin yanzu ya rike wannan mukami a baya, sannan yanzu haka Sani Abdulkadir Dambo babban jami’i mai binciken haraji ne a hukumar FIRS ta kasa.

Gwamnan Kano
Gwamnan Kano, Abba Gida Gida tare da Maniyyata Hoto: @EngrAbbaKYusif
Asali: Facebook

Bayani a kan

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Tsohon Sanatan PDP Ya Zama Babban Mai Yabon Gwamnatin Tinubu Dare da Rana

Dambo ya yi karatun digirinsa na farko ilmin Akanta daga jami’ar Bayero a garin Kano. Bayan nan sanarwar ta ce sabon shugaban ya na da digirgir.

Da farko Alhaji Dambo ya samu digiri na biyu a ilmin Akanta da tattalin kudi, daga baya ya sake yin wani digiri na biyun a kan kasuwanci (MBA).

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce shugaban na KIRS ya na cikin kungiyar malaman haraji na kasa, kuma ya fi shekara 20 ya na irin wannan aiki.

Sabon shugaba a SEMA

A yammacin Alhamis kuma aka ji cewa Alhaji Isyaku Abdullahi Kubarachi ya zama sabon shugaban hukumar SEMA mai bada agajin gaggawa.

Isyaku Abdullahi Kubarachi da Dambo za su fara aiki daga yau Juma’a, 16 ga watan Yuni 2023.

An nada Mukarrabai 14

A yau sai ga sanarwa cewa Abba Kabir Yusuf ya fitar da jerin Hadimai 14 da za su yi aiki da shi a matsayin masu bada shawara ko taimako na musamman.

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Tsohon Daraktan Ayyuka Na EFCC, Mohammed Abba

A rukunin SSA, Mai girma Gwamnan ya nada Dr. Sani Danjuma, Bello Nuhu Bello, Najeeb Bashir Nasidi, Dr. Abdurraman A. Kirare da kuma Safwan Garba.

Haka zalika sanarwar ta ce an nada Abdulkadir Balarabe Kankarofi da Salisu Yahaya Hotoro.

A rukunin SA, Salisu Muhammad Kosawa da Zulaihat Yusuf Aji za su rika aikin yada labarai, ta uku da aka nada ita ce a kujerar SA ita ce Rasheedat Usman.

Ahmad Aminu Yusuf, Ahmad Muhammad Gandu, Isa Muhammad Giginyu da Hassan Kabir sun zama PA a kan daukar hoto da dandalin sada zumunta.

Muhammadu Sanusi II a Aso Rock

A yammacin jiya ne aka ji labari Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II ya sa labule da Shugaban kasa, kuma ya fadi abin da su ka tattauna a kai

Khalifan ya ji dadin yadda Shugaba Bola Tinubu ya tunkari matsalar tattalin arzikin kasa ta hanyar janye tallafin fetur da kokarin farfado da darajar Naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng