Kotu Ta Bai Wa Yan Sanda, DSS Awa 48 Su Fito Da Motoccin Matawalle Da Suka Kwace
- A satin da ya gabata jami’an tsaro suka kai samame gidajen tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle tare da kwashe motoci da sauran kayayyaki bisa umarnin wata ƙaramar kotu
- Wata babbar kotun tarayya a jihar Zamfara ta umarci ‘yan sanda, DSS, da sauran jami’an tsaro da su fito da motocin da suka kwashe cikin sa’o’i 48
- Kotun ta bayar da wani umarni na wucin gadi da ke hana jami'an ɗaukar wani mataki na gaba kan lamarin har sai an saurari hukuncin da za ta yanke na gaba
Gusau, Zamfara – A ranar 9 ga watan Yuni ne jami’an tsaro suka kai samame gidajen tsohon gwamnan guda biyu na Gusau da na Maradun, inda suka kwashe motoci da sauran kayayyaki bisa umarnin wata karamar kotu.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, a ranar Alhamis ɗin nan, ta bayar da sabon umarni ga ‘yan sandan Najeriya, da ma’aikatan tsaron farin kaya, da sauran jami’an tsaron jihar.
Jami'an da kotun ta umarta kan batun motocin Matawalle
Umarnin ya shafi jami'an da suka yi ruwa da tsaki wajen kwashe motoci kusan 40 da wasu kayayyaki daga gidajen tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, da su dawo da su a cikin sa'o'i 48, kamar yadda ya zo a rahoton Channels TV.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A ranar 9 ga watan Yuni ne jami’an ‘yan sanda, DSS, da hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) suka dirarwa gidajen tsohon gwamnan na Gusau da na mahaifarsa Maradun, inda suka kwashe motoci da wasu kayayyaki bisa umarnin wata ƙaramar kotu a jihar.
Daga baya a wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce ta yi nasarar ƙwato motoci 40 daga samamen.
Kotu ta dakatar da jami'an tsaro daga ci gaba da ɗaukar mataki kan Matawalle
Sai dai a cikin wata ƙara mai lamba FHC/GS/CS/30/2023 da lauyan Matawalle, NS Na’Ige ya shigar a babbar kotun tarayya da ke Gusau, mai shari’a Aliyu Bappa, ya umarci waɗanda ake ƙara da su kawo mata dukkan motocin da suka kwashe a gidan Matawallen.
Haka nan kotun ta umarcesu da su zo da sauran kayayyakin da suka kwasa kuma a rubuce zuwa hannun kotun, sannan su jira har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan ƙarar a ranar 28 ga watan Yuni.
Kotun ta kuma bayar da umarni na wucin gadi na hana jami'an ‘yan sandan Najeriya, Sufeto janar na ‘yan sanda, kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, DSS, da NSCDC daga daukar wani mataki na gaba dangane da lamarin har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci.
Bello Matawalle ya yi martani kan samamen da jami'an tsaro suka kai gidansa
A wani labarin da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa, tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya yi zazzafan martani kan samamen da jami'an tsaron jihar suka kai gidajensa.
Matawalle ya yi iƙirarin cewa jami'an sun tafka masa sata a samamen, inda ya bayyana hakan a matsayin sakarci da talauci.
Asali: Legit.ng