Tsohon Sanatan PDP Ya Zama Babban Mai Yabon Gwamnatin Tinubu Dare da Rana
- Bisa dukkan alamu Ben Murray Bruce ya na jin dadin yadda Bola Ahmad Tinubu ya dauko mulkinsa
- Tsohon Sanatan ya na da kusanci da Atiku Abubakar, hakan bai hana shi yabon gwamnati mai-ci ba
- Tun da Tinubu ya zama shugaban kasa, Bruce yake yin magana a Twitter, ya na mai jinjina masa
Abuja - A ‘yan kwanakin da yayi a kan kujerar shugaban kasa, Mai girma Bola Ahmad Tinubu ya na ta samun yabon Ben Murray Bruce.
A ranar Laraba, Sanata Ben Murray Bruce ya yi amfani da shafinsa na Twitter ya na mai yabon matakan da Gwamnatin Bola Tinubu ta dauka.
Jagoran jam’iyyar adawar ta PDP ya ce a kan Tinubu aka fara yin shugaban kasar da ya san harkar kasuwanci, saboda haka yake hango cigaba.
An cire bambancin farashin kudin waje
Bruce wanda ya taba wakiltar gabashin Bayelsa a majalisar dattawa, ya ce karshen masu kasuwancin bogi ya zo karshe a mulkin Tinubu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Bola Tinubu ne shugaban kasa na farko a Najeriya da yake da masaniya kan tattalin arziki. Bari in fadawa ‘yan kasuwancin 419 gaskiya.
Lokacin shiga Aso Rock cikin dare domin samun iznin shigo da kaya daga kasashe waje ko yafiyar haraji ko kasuwancin boge ya zo karshe.
Ku maida hankali a kan kasuwanci na hakika. Tinubu ba zai yi son rai kamar tsofaffin shugaban kasa ba. Wannan karo dole sai kun dage.
- Ben Murray Bruce
Bruce ya fara jawo magana a Twitter
Kafin nan an ji ‘dan kasuwar ya na cewa sabon shugaban kasar za bunkasa tattalin arzikin Najeriya. Hakan ya jawo surutu a dandalin Twitter.
Tun a ranar da aka rantsar da Bola Ahmed Tinubu, Legit.ng Hausa ta fahimci tsohon Sanatan ya ajiye rigar siyasarsa a gefe, ya na tayi shi murna.
Duk da ya na da kusanci da ‘dan takaran PDP a zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar, Sanata Bruce ya yi farin cikin ganin Tinubu a mulki.
A dogon bayanin da ya yi a dandalin Twitter, Sanatan ya kira shugaban da cikakken ‘dan Najeriya mai kishin kasa, a karshe ya zuba masa addu’o’i.
Bayan zaben 'yan majalisa, ‘dan siyasar ya taya Godswill Akpabio da Tajuddeen Abbas murna, hakan ya nuna ya ajiye sabanin siyasarsa a gefe.
Rawar G5 a zaben Majalisa
An samu labarin cewa Nyesom Wike da mutanensa na G5 sun taimaka wajen samun nasarar Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas a zaben ‘yan majalisa.
Wike, Seyi Makinde Samuel Ortom, Ifeanyi Ugwuanyi da Okezie Ikpeazu sun zama matsala a PDP. ‘Yan siyasar sun taimaka wajen doke Atiku Abubakar.
Asali: Legit.ng