Tinubu Ya Lallaba a Asirce, Ya Roki Sanatoci - Sanata Ya Fadi Yadda Akpabio Ya Ci Zabe

Tinubu Ya Lallaba a Asirce, Ya Roki Sanatoci - Sanata Ya Fadi Yadda Akpabio Ya Ci Zabe

  • Muhammad Ali Ndume ya nuna ba a banza kurum Godswill Akpabio ya zama shugaban majalisa ba
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga, ya fita har ‘Dan majalisar na Akwa Ibom ya samu nasara
  • Sanata Ndume yke cewa Shugaban Najeriya ya je waen wasu Sanatoci, ya roke su da su bi bayan Akpabio

Abuja - Muhammad Ali Ndume mai wakiltar mazabar Kudancin Borno a majalisar dattawa, ya yi karin haske a kan nasarar da Godswill Akpabio ya samu.

Da aka yi hira da shi a tashar Channels a ranar Talata, Muhammad Ali Ndume ya ce Bola Ahmed Tinubu ya taimaka wajen ganin nasarar Godswill Akpabio.

Sanatan yake cewa Mai girma shugaban kasa ya ziyarci wasu Sanatoci, kuma ya shawo kan su cewa su marawa Sanata Akpabio baya ya jagorance su.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Kai Ni Wajen Bola Tinubu – Jonathan a Kan Ziyararsa Zuwa Aso Rock

Bola Tinubu da Akpabio
Bola Tinubu ya hadu da Godswill Akpabio Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Ndume ya kuma shaida cewa sabon shugaban majalisar dattawa ya cancanci wannan kujera.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rawar da Shugaba Tinubu ya taka

“Jam’iyya da Shugaban kasa ta na da ‘dan takarar da ta ke so. Saboda shugaban kasa kwararren ‘dan siyasa ne, ya san dawar garin sosai.
Ya tura mutanensa domin ba mu gudumuwa. Kuma hakan ya yi tasiri. Mataimakin shugaban kasa (Kashim Shettima) ya na layin nan.
Shi kan shi ya kira wasu mutane. Shugaban kasa ya lallaba ya ziyarci wasu mutane kuma ya roke su da su zabi Sanata Godswill Akpabio.
Kuma ya na da dalilansa. Dalilansa masu gamsarwa ne. Da farko ya ce a bar ‘Yan kudu maso kudu domin tun 1999 ba su hau kujerar ba."

- Muhammad Ali Ndume

Karfin jam'iyya a zaben Majalisa

The Cable ta rahoto Ndume ya na cewa a zaben 2019 da ya nemi takarar wannan kujera, bai kai ko ina ba domin jam’iyya ta na goyon Ahmad Lawan.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sa Labule da Sabon Shugaban Majalisar Dattawa, Gwamnoni 2 da Ganduje, Bayanai Sun Fito

Abin da ya faru kenan a wannan karo, APC ta goyi bayan Sanata Akpabio a kan Abdulaziz Yari.

A hirar da aka yi da shi jiya a gidan talabijin, Sanatan na APC bai kama sunayen wadanda Mai girma Bola Tinubu ya roka su goyi bayan Akpabio ba.

Majalisar dokokin Kaduna

Idan mu ka koma wani rahoton, za a ji tsohon shugaban majalisar dokokin Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Ibrahim Zailani ya saki wasu bayanai da ba a sani ba.

‘Dan majalisar na Igabi ta yamma ya ce an nemi soke kotun shari’a da na gargajiya a Kaduna a lokacin gwamnatin Nasir El-Rufai, amma sai su ka hana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng