Shugaban INEC Na Kasa Zai Bayar Da Shaida a Gaban Kotu a Karar Atiku Kan Nasarar Shugaba Tinubu
- Lauyoyin Atiku Abubakar sun gayyato shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) domin bayar da shaida a gaban kotu
- Farfesa Mahmood Yakubu zai bayar da shaida a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a ranar Alhamis
- Shugaban na hukumar INEC zai kuma gabatar da wasu muhimman takardun zaɓe a gaban kotun mai alƙalai biyar
Abuja - Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, zai bayar da shaida a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ranar Alhamis, cewar rahoton Premium Times.
Yakubu zai bayar da shaida ne a ƙarar da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP ya shigar, inda yake ƙalubalantar nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya yi a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya
Atiku, ya zargi hukumar INEC da Shugaba Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da yin maguɗi a zaɓen.
Babban lauyansa, Chris Uche, ya gayawa kotun mai alƙalai biyar a ranar Talata cewa Farfesa Yakubu zai bayyana a gabanta ranar Alhamis.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Farfesa Mahmood zai bayar da shaida kan nasarar Tinubu a kotu
A bisa roƙon da lauyoyin Atiku suka yi, an gayyato Farfesa Mahmood Yakubu domin ya bayar da shaida akan zaɓen wanda ake ta taƙaddama a kansa.
Haka kuma, ana saran zai bayar da wasu muhimman takardun zaɓe waɗanda za su taimaka wa ƙarar da Atiku yake yi, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Mr Uche, wanda yake babban lauya ne ya sanar da lauyoyin INEC, Shugaba Tinubu da APC dangane da zuwan Mahmood da aka tsara domin hana aukuwar wani abinda zai iya kawo wa zaman kotun cikas.
Tinubu Ya Lallaba a Asirce, Ya Roki Sanatoci
A wani labarin na daban kuma, kun ji yadda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya lallaba ya gana da wasu sanatoci a keɓance domin Sanata Akpabio ya samu nasara a zaɓen majalisar dattawa ta 10.
Sanata Ali Ndume shind ya bayyana hakan inda ya ce Shugaba Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Sanata Godswill Akpabio ya yi masara a zaɓen.
Asali: Legit.ng