Mata Zalla Za Su Rike Mukamin Mataimakan Shugabannin Kanananan Hukumomi, Gwamnan Neja, Umar Bago
- Gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago, ya yi alƙawarin cewa dukkan mataimakan shugabannin ƙananan hukumomi a jihar za su kasance mata a lokacin mulkinsa
- Bago ya yi nade-nade biyar a baya-bayan nan, waɗanda dukkansu maza ne, amma ya shirya naɗa mata biyar a gaba domin tabbatar da daidaito a gwamnatin tasa
- Gwamnan ya jaddada ƙudirin gwamnonin jam’iyyar APC, na goyon bayan nasarar shugaba Bola Tinubu, ya kuma yi magana kan batun ‘yan fashi daji da suka addabi a jihar
Abuja - Gwamnan jihar Neja, Umar Bago Mohammed, a ranar Talata ya ce dukkan mataimakan shugabannin ƙananan hukumomin za su kasance mata ne a gwamnatinsa.
Gwamnan ya kuma ce akwai naɗe-naɗe guda biyar da ya yi waɗanda dukkansu maza ne, amma akwai naɗe-naɗe biyar masu zuwa da za su kasance mata, kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Umar Bago ya ce gwamnatinsa za ta daidaita mata da maza wajen muƙamai
Ya kuma bayar da tabbacin cewa ba za a samu banbance-banbance tsakanin maza da mata ba, domin za a riƙa raba muƙaman siyasa daidai wa daida tsakanin maza da mata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A rahoton jaridar Nigerian Tribune, gwamnan ya ce akwai yiwuwar a raba muƙamai rabi da rabi tsakanin maza da mata a jihar.
Ya bayyana hakan ne bayan fitowa taron da ƙungiyar gwamnonin APC suka yi da Tinubu, domin taya shi murnar nasarar zaben shugabannin majalisar dokokin tarayya ta 10 da aka yi.
Bago ya ƙara da cewa burin duka gwamnonin jam’iyyar APC, shi ne tabbatar da samun nasarar gwamnatin Shugaba Tinubu.
Da yake amsa tambayoyi kan yadda zai tunkari ƙalubalen ‘yan fashin daji da suka addabi jihar ta Neja, Gwamna Bago ya ce akwai wuraren da suke a hannun 'yan ta'adda saboda faɗin da jihar take da shi, amma yana tattaunawa da jami'an tsaro kan yadda za a shawo kan lamarin.
Babu wata ƙaramar hukuma da ke hannun 'yan bindiga
Gwamnan ya musanta zargin da ake na cewa wasu ƙananan hukumomin jihar na karkashin ikon ‘yan fashin ne, inda ya ce:
“Ba mu da wata ƙaramar hukuma da ke hannun ‘yan bindiga a yanzu, sai dai akwai ‘yan fashin a wasu ƙananan hukumomin.”
Ya alaƙanta ayyukan ‘yan bindiga a jihar da faɗin ƙasa da jihar ke da shi, yana mai jaddada cewa Neja ta yi iyaka da ƙasashen waje, da wasu jihohin ƙasar da makiyaya ke shigowa ta cikinsu.
Gwamnan Katsina ya kwace filayen da gwamnatin baya ta rabar
Legit.ng ta kawo muku rahoto a baya kan yadda sabuwar gwamnatin jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Dikko Umar Radda, ta sanar da ƙwace filayen da gwamnatin Aminu Masari ta rabawa mutane.
Sanarwar na ƙunshe ne a wata takarda da Ado Yahaya, daraktan albarkatun ƙasa na jihar Katsina ya fitar ta ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar.
Asali: Legit.ng