Bilyaminu Moriki Ya Zama Sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara
- Majalisar dokokin jihar Zamfara ta zaɓi sabon kakaki da mataimakinsa waɗanda za su ja ragamar shugabancinta
- Hon. Bilyaminu Moriki da Hon. Adamu Aliyu sun zama sabbin shugabannin majalisar dokokin ta bakwai a jihar
- Dukkaninsu su biyun an zaɓe su ne ba tare da abokan hamayya ba a majalisar wacce jam'iyyar PDP ke da rinjaye
Jihar Zamfara - Majalisar dokokin jihar Zamfara ta zaɓi Bilyaminu Ismail Moriki daga Zurmi ta Arewa a matsayin sabon kakakinta.
Majalisar dokokin jihar ta kuma zaɓi Adamu Aliyu daga mazaɓar Gummi ta biyu a matsayin mataimakin kakakinta, a lokacin ƙaddamar da ita a ranar Talata, 13 ga watan Yunin 2023, cewar rahoton Tribune.
Kakakin da mataimakinsa sun ɗare kan kujerunsu ne bayan ɗan majalisa mai wakiltar Gummi ta ɗaya, Hon. Bashar Aliyu Gummi ya zaɓe su inda Hon. Nasiru Abdullahi daga Maru ta Arewa ya mara masa baya.
Sanata Barau Jibrin: Muhimman Abubuwan Sani 5 Dangane Da Sabon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa
Rahotanni sun tabbatar da kakakin da mataimakinsa an zaɓe su ne ba tare da abokan hamayya ba bayan an yarda su ɗare kan muƙaman.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Magatakardan majalisar dokokin Shehu Saidu Anka, shine ya jagoranci ƙaddamar da majalisar, inda ya buƙaci sabon kakakin da ya rantsar da sauran ƴan majalisar bayan ya yi rantsuwar kama aiki.
Jam'iyyar PDP ke da rinjaye a majalisar dokokin
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara tana da kujeru 17 cikin 24 na majalisar dokokin jihar, inda jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai adawa a jihar ta ke da kujeru bakwai.
Gwamnan jihar Dauda Lawal Dare, ya samu wakilcin mataimakinsa Mani Mallam Mumuni, a wajen ƙaddamar da majalisar inda yaje a matsayin mai sanya idanu.
Sauran manyan mutanen da suka halarci ƙaddamar da majalisar dokokin jihar ta bakwai, sun haɗa da sarakunan gargajiya, ƴan siyasa da manyan ƙusoshi a jihar.
Sabon Ɗan Majalisa Ya Lashe Zaben Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Plateau
Rshoto ya zo cewa majalisar dokokin jihar Plateau ta yi sabon ango, majalisar ta zaɓi Moses Sule a matsayin sabon kakakinta.
Moses Sule dai wannan shi ne karonsa na farko a majalisar dokokin ta jihar Plateau, inda daga zuwa har ya zama kakaki.
Asali: Legit.ng