TJ Abbas: Abubuwa 6 Dangane da Tarihi, Ilmi da Siyasar Shugaban Majalisar Wakilai
- Tajuddeen Abbas PhD mai wakiltar mazabar Zariya ya lashe zaben shugaban majalisar wakilai
- ‘Dan majalisar ya samu kuri'u 353, ya yi galaba a kan Ahmed Idris Wase da kuma Aminu Sani Jaji
- Hon. Tajuddeen Abbas kwararren ‘dan siyasa ne kuma ‘dan boko, sannan jinin sarauta ne a Zazzau
Mun kawo bayani a game da rayuwa, siyasa da zaman Tajuddeen Abbas a majalisa.
1. Haihuwar Tajuddeen Abbas
A ranar 1 ga watan Oktoban 1963 aka haifi ‘dan majalisar na mazabar Kewaye, za a rantsar da shi a a majalisa ya na mai shekaru 59 a Duniya.
2. Karatun Boko
Bayanan da aka samu a shafin Zagezage a yau ya nuna Abbas Tajuddeen ya samu shaidar Grade II ta malanta a makarantar KTC Katsina a 1981.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tajuddeen yi digirin farko a Jami'ar Ahmadu Bello a Zaria a bagaren kasuwanci, ya samu shaida a 1988. Daga nan sai ya koma yin digirgir a 1993.
A shekarar 2010 ne ‘dan majalisar ya kammala digirinsa na uku watau PhD duk a harkar kasuwanci daga Jami'ar Usmanu Danfodio da ke garin Sokoto.
3. Aiki a makarantu da kamfani
Sabon shugaban majalisar ya taba zama malamin makarantan firamare daga shekarar 1981 zuwa 1988. Bayan nan ya zama malami a kwalejin Nuhu Bamalli.
A 1993 ne ya bar Nuhu Bamalli Polytechnic, ya karbi aikin Manajan kasuwanci a kamfanin NTC PLC. Bayan nan sai ya zama malamin jami’a a KASU a 2005.
4. Shiga siyasa da majalisar Tarayya
Bayan shekaru biyar Tajuddeen ya ajiye aikin jami’a, a 2011 ya shiga takara kuma ya yi nasarar zama zababben ‘dan majalisa mai wakiltar mazabar Zariya.
‘Dan siyasar ya lashe zaben sa a 2015, 2019 da kuma 2023 duk a karkashin jam'iyyar APC mai mulki.
5. Kudirori da gogewa a Majalisa
Vanguard ta ce a majalisa shi ya fi kowa kudiri a majalisa tsakanin 2015 da 2019. Haka zalika a majalisa ta tara, ya zarce kowa, ya na da kudiri 74.
A majalisa ta goma, Dr. Tajudden Abbas ya yi aiki a kwamitocin kasuwanci, kudi, ayyuka na musamman, tsaro, tsare-tsaren kasafin kudi da tattali.
Makonni kadan kafin ya zama shugaban majalisar wakilai, kwamitin sufuri ta kasa yana karkashinsa.
6. Iyan Zazzau
A shekarar 2021 Sarkin Zazzau, Amb. Ahmad Nuhu Bamalli ya nada Abbas Tajuddeen a matsayin Iyan Zazzau, ya canji Marigayi Alhaji Bashir Aminu.
‘Dan majalisar ya gaji sarautar kakansa, Iya Abdullahi Musa wanda ‘da ne a wajen Sarkin Zazzau, Malam Musa da ya yi mulki daga gidan Mallawa.
Nasara a zaben Majalisa
Majalisa Ta 10: Tsohon Minista Ya Ce Kirista Dan Kudu Ya Dace Ya Gaji Kujerar Lawan, Soki Sauran Masu Nema
An samu labarin yadda Hon. Tajudeen Abbas mai wakiltar mazabar Zariya a jihar Kaduna ya samu kuri'u 353 a zaben da aka gudanar a majalisa.
'Dan takaran na APC ya lallasa sauran abokan adawarsa; Ahmad Wase da Aminu Jaji.
Asali: Legit.ng