Emefiele Ya Jawo Aka Yi Mani Daurin Kwanaki 101 Saboda Fallasa Badakalar $3bn

Emefiele Ya Jawo Aka Yi Mani Daurin Kwanaki 101 Saboda Fallasa Badakalar $3bn

  • George Uboh ya zargi Godwin Emefiele da bada umarnin a tsare shi saboda ya nemi ya tona asiri
  • ‘Dan kasuwar ya ce a 2019 ya yi kokarin fallasa yadda ake cuwa-cuwar canjin kudi a bankin CBN
  • A karshe aka tsare Uboh na kwanaki fiye da 100, a cewarsa laifinsa shi ne neman tona asirin Emefiele

Abuja - Shugaban kungiyar George Uboh Whistleblowers Network, George Uboh, ya saki wasu maganganu bayan an dakatar da Godwin Emefiele.

Daily Trust ta rahoto Dr. George Uboh ya na ikirarin cewa fallasa badakalar canjin kudi da ya yi, ya jawo an tsare shi na kwanaki 101 a shekarar 2019.

Shugaban kungiyar GUWN ya bayyana haka ne a lokacin da ya tara manema labarai, ya zanta da su a babban birnin tarayya Abuja a yammacin Litinin.

Kara karanta wannan

A bar batun Emefiele: Jam'iyyar su Peter Obi ta fadi hukumar da ya kamata a bincika a Najeriya

Emefiele
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A jawabin da ya yi, Dr. Uboh ya yabi Bola Tinubu game da dakatar da gwamnan bankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Badakalar $3bn a CBN?

Yayin da gidajen yada labarai cike su ke da labarin cafke Emefiele da abin da ya biyo baya ko kafin nan da rashin gaskiyarsa, amma ‘Dan Najeriyan da ya isa ya soki Emefiele.
Kungiyar George Uboh Whistleblowers Network watau GUWN ta fallasa rashin gaskiyar Emefiele a game da abin da ya shafi badakalar canjin kudin fiye da fam $3bn.

- Dr. George Uboh

Uboh yake cewa ya tona asirin abubuwan da ke faruwa a CBN ne a wasu jeringiyar wasikun da ya rika aikawa gwamnan babban bankin a Afrilun 2019.

'Yan sanda sun cafke Uboh

15 ga watan Mayun 2019, ranar da Emefiele zai je gaban Sanatoci domin tantance shi, ya shiga wa’adina na biyu, sai aka cafke ni a ofishina a Maitama.

Kara karanta wannan

CBN ta zama ATM din munafukan gwamnati: Shehu Sani ya bi ta kan korarren gwamna Emefiele

An tsare ni na tsawon kwanaki 101 da sunan bata sunan Emefiele. Babban Alkalin kotun birnin tarayya a lokacin Ishaq Bello ya ki sauraron neman beli ba.
DIG Mike Ogbizi da bakinsa ya hana a bani beli duk da na cika sharudan samun beli a ofishin CID."

- Dr. George Uboh

Shawara zuwa ga Tinubu

Punch ta rahoto ‘dan kasuwan ya na kira ga Bola Ahmed Tinubu, GCFR ya hada-kai da ‘yan tonon silili domin a bankado irin badakalar da aka tafka a kasar.

Uboh ya kuma bada shawarar a karfafa tsarin nan da Muhammadu Buhari na tonon silili, wannan karo ya ce ka da a jefa ofishin a karkashin wani Minista.

El-Rufai da tikitin Musulmi da Musulmi

An ji labari International Society for Civil Liberties and Rule of Law ta bukaci a cafke tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai saboda kalamansa.

A faifen murya ko bidiyo, kungiyar ta ce tsohon Gwaman Kaduna ya na kurin nasarar maida Kaduna kasar musulunci, haka kuma aka yi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng