Majalisa Ta 10: Jam'iyyar PDP Ta Bayyana 'Yan Takarar Da 'Yan Majalisunta Za Su Zaba

Majalisa Ta 10: Jam'iyyar PDP Ta Bayyana 'Yan Takarar Da 'Yan Majalisunta Za Su Zaba

  • Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa ba za ta gayawa ƴan majalisunta wanda za su zaɓa a shugabancin majalisa ba
  • Jam'iyyar tace ƴan majalisunta na da ikon cin gashin kansu wajen zaɓar ƴan takarar da suka kwanta musu a zaɓen
  • PDP tace ta cimma matsaya kan shugabancin majalisa ta 10 amma ba za ta bayyana hakan ga duniya ba

Abuja - A yayin da ake tunkarar zaɓen shugabannin majalisa ta 10 a sati mai zuwa, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta bayyana cewa ba ta yarda ta matsawa ƴan majalisunta lamba kan wanda za su zaɓa ba.

Jam'iyyar adawan ta kuma zargi jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na yi wa ƴan majalisu barazanar cafkesu domin tilasta musu su zaɓi wasu ƴan takara, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Yarjejeniyar Da Aka Cimma Tsakanin Shugaba Tinubu Da Akpabio Kan Shugabancin Majalisar Dattawa

PDP ba za ta tilasta 'yan majalisunta zabar wasu 'yan takara a shugabancin majalisa ta 10
PDP tace 'yan majalisun na da 'yancin zaben wanda suke son zaba Hoto: Tribune.com
Asali: UGC

Kakakin jam'iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba, shi ne ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da manema labarai a sakatariyar jam'iyyar da ke a birnin tarayya Abuja, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Sai dai ya kuma ƙara da cewa jam'iyyar PDP ta san matsayar da ta cimma kan shugabancin majalisar wanda ba sai ta bayyana ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ƴan majalisun PDP sai sun zaɓa sun darje

Da aka tambaye shi ko jam'iyyar za ta yi katsalandan kan yadda ƴan majalisunta za su kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen, ya bayyana cewa jam'iyyar ba wannan bane a gabanta.

"Mun bayyana cewa jam'iyyarmu tana son ci gaban dimokuraɗiyya da raba mulki da ikon cin gashin kowane ɓangare na gwamnati. Amma tabbas su yi aiki tare ta yadda za su yi aiki wajen ci gaban al'umma." A cewarsa

Kara karanta wannan

Mummunar Gobara Ta Tashi a Wata Babbar Kasuwa a Jihar Yobe, An Tafka Gagarumar Asara

"Mu a jam'iyyance bamu yarda da mu je mu gayawa ƴaƴan jam'iyyar ku yi wannan ku yi wancan ba. Amma kamar yadda na faɗa a baya, a jam'iyyance mun san matsayar da mu ka cimmawa kan muƙaman."

Shettima Ya Janyo Jankalin Zababbun Sanatoci

A wani labarin na daban kuma, mataimakin shugaban ƙasa Ƙashim Shettima ya yi kira mai jan hankali kan zaɓaɓɓun sanatoci.

Shettima ya buƙaci zaɓaɓɓun sanatocin waɗanda za a ƙaddamar nan gaba kaɗan da su kawar da kansi daga amsar na goro a wajen ƴan takarar da ke neman shugabancin majalisar.

Mataimakin shugaban ƙasar ya yi nuni da cewa zaman lafiyar ƙasa ya fi abinda za su samu a aljihunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng