Jam'iyyar NNPP Ta Fusata, Ta Yi Martani Mai Zafi Kan Ganduje Bisa Barazanar Marin Kwankwaso

Jam'iyyar NNPP Ta Fusata, Ta Yi Martani Mai Zafi Kan Ganduje Bisa Barazanar Marin Kwankwaso

  • Jam'iyyar NNPP a jihar Osun ta yi martani mai zafi barazanar da tsohon gwamnan Kano, Ganduje ya yi ta marin Kwankwaso
  • Jam'iyyar tace furucin na Ganduje ya yi muni kuma bai kamata su fito daga bakin tsohon gwamnan na jihar Kano ba
  • NNPP ta ja kunnen Ganduje da kada ya kuskura ya aikata abinda ya yi barazanar yi idan ba haka ba zai haɗu da fushinta

Jihar Osun - Shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Osun, Dr Tosin Odeyemi, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kan barazanar marin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Odeyemi, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar a birnin Osogbo, ya ƙalubalanci Ganduje da ya aikata abinda ya yi barazanar yi akan Kwankwaso ya ga abinda zai faru da shi, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Wane Mutum: Kwankwaso Ya Mayar Da Martani Mai Zafi Kan Barazanar Marin Da Ganduje Ya Yi Masa

Jam'iyyar NNPP ta yi martani mai zafi ga Ganduje
Jagoran jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Aminiya.com
Asali: UGC

A ranar Juma'a ne bayan Ganduje ya kammala ganawa da shugaba Tinubu, ya gayawa ƴan jarida cewa rusau ɗin da gwamnatin Abba Gida-Gida ta ke yi a Kano ba bisa ƙa'ida bane.

Ya kuma bayyana cewa duk da yasan cewa Kwankwaso yana cikin Villa a lokacin, da ya sharara masa mari idan suka haɗu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NNPP ta caccaki Ganduje

Da yake martani kan kalaman Ganduje, Odeyemi ya bayyana cewa Ganduje bai kamata ya yi wannan furucin ba, inda ya ƙara da cewa hakan ya nuna yadda ya yi taɓargaza lokacin da yake mulkin jihar Kano, rahoton The Sun ya tabbatar.

A kalamansa:

"Ta yaya tsohon gwamna sukutun da guda zai yi wannan furucin? Yana tunanin cewa har yanzu muna cikin zamanin da ba a hukunta rashin ɗa'a a Najeriya?"

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Fadi Abin da Ya Shaidawa Tinubu Bayan Ganduje Ya Yi Barazanar Marinsa

"Kamata ya yi Ganduje ya je ya huta. Ya fara kafa daular siyasa kamar yadda jagoranmu Kwankwaso ya yi. Idan kuma har yana son ya ƙure haƙurin ƴan NNPP a Najeriya, to yaje ya aikata barazanar da ya yi. Idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira."

Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Barazanar Ganduje

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Ƙwankwaso. ya yi martani kan barazanar marinsa da Abdullahi Umar Ganduje ya yi masa.

Kwankwaso ya bayyana cewa Ganduje a ruɗe yake shiyasa yake ta faɗin wannan soki burutsun na cewa zai mare shi.

Tsohon gwamnan ya ce Ganduje yaronsa ne a siyasa wanda ko ƙwayar idonsa ba zai iya kallo ba idan suka haɗu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng