Abubuwa 4 Da Emefiele Ya Yi Da Suka Bata Wa Tinubu, Gwamnoni, Da Sauran 'Yan Najeriya Rai

Abubuwa 4 Da Emefiele Ya Yi Da Suka Bata Wa Tinubu, Gwamnoni, Da Sauran 'Yan Najeriya Rai

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni, ya bayar da sanarwar dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Sanarwar ta ce, dakatarwar da aka yi wa gwamnan babban bankin, ta biyo bayan binciken da ake yi a ofishinsa da kuma sauye-sauyen da ake shirin yi a fannin hada-hadar kudi.

Emefiele dai ya samu muƙamin gwamnan CBN ɗin ne a shekarar 2014, biyo bayan tsige Sunusi Lamido Sanusi da shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi watanni kaɗan kafin karewar wa’adinsa.

Emefiele ya fusata 'yan Najeriya da tsarukansa
Abubuwan da Emefiele ya fusata 'yan Najeriya da su. Hoto: Central Bank Of Nigeria, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kafin zamansa gwamnan CBN, Emefiele ya kasance Manajan Daraktan bankin Zenith.

Emefiele ya fuskanci suka daga wurin ‘yan Najeriya, saboda yadda yake tafiyar da harkokin tattalin arziƙin da kan jefa 'yan ƙasar cikin yanayi.

Kara karanta wannan

DSS Ta Jero 'Laifuffukan' Emefiele, Za Ta Bukaci Karin Lokacin Cigaba da Tsare Shi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng ta yi nazari wajen tattaro muku manyan dalilan da suka sa sabuwar gwamnatin da Tinubu ke jagoranta ɓullowa Emefiele ta wannan fuska.

1. Tabarbarewar tattalin arziki

Tsarukan da Emefiele ya kawo a babban bankin basu yi wa ‘yan Najeriya da dama daɗi ba, ciki kuwa har da wasu fitattun gwamnoni da wasu masu fada aji a ƙasar.

A lokacin wa'adinsa, kuɗin Najeriya, wato naira, ta samu koma baya matuƙa, inda a yanzu haka ake siyar da ita a kan farashi sama da N750 kan kowace dala ɗaya a kasuwannin bayan fage.

Naira a farashin gwamnati na nan a kan N462.9 kan kowace dala kamar yadda yake a farashin CBN na yammacin ranar Alhamis.

2. Batun sake fasalin kuɗin Najeriya

A ƙarshen shekarar 2022, CBN ya ɓullo da wani tsari na sake fasalin Naira wanda ya sha suka saboda rashin tabbas da kuma matsalolin da ya haifar a faɗin Najeriya.

Kara karanta wannan

CBN ta zama ATM din munafukan gwamnati: Shehu Sani ya bi ta kan korarren gwamna Emefiele

Ana cikin kakar yaƙin neman zaɓe, Bola Tinubu, ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki a lokacin, ya yi iƙirarin cewa tsarukan da CBN ta kawo, dominsa aka kawo su.

Ya ce batun iyakance cire N20,000 a kowace rana da kuma N100,000 a kowane mako, da gangan aka kawo tsarin don a hana shi damar lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

A ranar 13 ga watan Maris ne aka dakatar da aiwatar da tsarin CBN na sake fasalin kuɗin Najeriya, biyo bayan koma bayan tattalin arzikin da aka samu a watanni uku na farkon shekarar da muke ciki.

3. Batun karancin Naira

Taƙaita adadin sabbin takardun kuɗaɗe da ke yawo, kwanaki kaɗan kafin cikar wa'adin 31 ga watan Janairu, da bankin ya ƙayyade na daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi, ya bar wa 'yan Najeriya tabon da har yanzu suke jinyarsa.

Kuɗaɗen da dokar ta shafa a lokacin sun haɗa da N1000, N500 da N200, wanda babban bankin ya sauyawa fasali.

Kara karanta wannan

Da sauran rina a kaba: Sowore ya bayyana sunayen abokan cin mushen Emefiele

Sai da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu, Bola Tinubu ya shawarci babban bankin kasar, da ya bari a ci gaba da amfani da tsofaffi da sababbin kuɗaɗen tare har na tsawon watanni 12.

Ana cikin wannan takun saƙa ne aka jiyo wasu fitattun ‘yan Najeriya, wasu masu faɗa a ji, da wasu ƙungiyoyin farar hula sun yi kira da a kama Emefiele tare da gurfanar da shi gaban ƙuliya.

A watan Maris, fitacciyar kafar yaɗa labarai ta Najeriya, Premium Times, ta yi kira da a kama gwamnan babban bankin kasar tare da gurfanar da shi gaban kotu.

Jaridar ta yi wannan kiran ne saboda irin tsauraran tsarukan da babban bankin ya kawo ƙarƙashin jagorancin Emefiele.

4. Tsayawar Emefiele takarar shugaban ƙasa

Emefiele ya fuskanci kakkausar suka, sakamakon shiga siyasa da aka ga ya yi, inda ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

"Bai Kamata Tinubu Ya Iya Dakatar Da Emefiele Ba": Fitaccen Lauya Ya Bayyana

Duk da cewa gwamnan ya yi kokarin karyata batun shigar tasa siyasa, magoya bayansa sun yi ta kiraye-kiraye kan a tsayar da shi takara a jam’iyya mai mulki.

Masana da dama sun nuna cewa bai kamata wanda ke riƙe da shugabancin CBN, ya nuna wani ra'ayi da yake da shi na siyasa ba.

Shehu Sani ya yabi Tinubu kan dakatar da Emefiele

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji cewa tsohon sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya yabawa matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Idan baku manta ba, sanarwar dakatar da gwamnan babban bankin, Mista Godwin Emefiele ta zo ne da yammacin ranar Juma'a 9 ga watan Yunin da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng