Mun Kwato Motoci Masu Tsada 40 a Gidan Matawalle, Gwamnatin Zamfara
- Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da cewa 'yan sanda sun kai samame gidan tsohon gwamna, Bello Matawalle
- A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Suleiman Idris, ya fitar, ya ce sun kwato motoci 40 yayin samamen
- A cewar sanarwan, 'yan sanda sun ɗauki wannan matakin ne bisa umarnin da Kotu ta bayar
Zamfara - Jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya da haɗin guiwar DSS sun kai samame gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, na Gusau.
Mai magana da yawun gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, Suleiman Idris, ya tabbatar da haka, inda ya bayyana cewa sun kwato kadarorin gwamnati yayin samamen.
Gwamnatin Zamfara ta ce jami'an tsaron sun kwato Motocin hawa 40, daga ciki harda motocin sulƙe uku da SUV guda 8, yayin wannan samame, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Meyasa jami'an tsaro suka dira gidan Matawalle?
Sanarwan da Idris ya fitar ta bayyana cewa gwamnati ta samu umarni daga Kotu na bincikar gidan tsohon gwamnan, bisa haka ne jami'an tsaro suka mamaye gidan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A rahoton Tribune, Wani sashin sanarwan ya ce:
"Gwamnatin Zamfara ta yi karin haske kan samamen da 'yan sanda suka kai gidan tsohon gwamnan da ya sauka, Bello Matawalle, inda suka kwato Motocin da ake zargin ya wawure."
"Da safiyar Jumu'a, 'yan sanda suka dira gidan tsohon gwamnan kuma suka ci karo da motoci 40. Sun shiga gidan Matawalle bisa umarnin Kotu wanda ta amince a gudanar da bincike."
"Idan baku manta ba tun da fari, gwamnatin Zamfara ta tura sako a hukumance ga tsohon gwamna, Bello Matawalle, da mataimakinsa su dawo da motocin da suka wawure cikin kwanakin aiki 5."
Daga karshe, sanarwan ta yi kira ga ɗaukacin mutanen jihar Zamfara su kwantar da hankulansu yayin gwamnati ke kokarin magance matsalar tsaro da ƙarancin ruwan sha a faɗin jihar.
Gwamnatin Kano Za Ta Cigaba da Rushe-Rushe Bayan Rade-Radin Tilasta Dakatarwa
A wani labarin kuma Gwamnatin Abba Gida-Gida a Kano ta ce zata ci gaba da rusau kamar yadda ta fara kuma rahoton cewa an dakatar da ita ba gaskiya bane.
Ga dukkan alamu gwamnatin Kano zata ruguza gidaje, shaguna da ginin da su ke masallatai, makarantu, makabartu da wasu asibitoci.
Asali: Legit.ng