Kwankwaso Ya Fadi Abin da Ya Shaidawa Tinubu Bayan Ganduje Ya Yi Barazanar Marinsa
- Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayanin yadda ganawarsa da Bola Ahmed Tinubu ta kasance a Aso Rock
- Tsohon Gwamnan na Kano ya zargi magajinsa da tattara kadarorin al’umma, ya mallakawa iyalinsa
- Kwankwaso ya wanke gwamnatin NNPP ne bayan da Abdullahi Ganduje ya kai korafi kan Abba Yusuf
Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cika da mamaki da ya ji abin da ya faru a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.
The Cable ta ce Rabiu Musa Kwankwaso ya shaida cewa ya yi wa Mai girma shugaban kasa bayanin yadda gwamnatin Ganduje ta rika tafka barna.
Hakan ya na zuwa ne bayan tsohon Gwamnan ya kai korafin sabuwar gwamnatin NNPP a Kano, a dalilin haka Bola Tinubu ta zauna da kowane bangare.
Da yake bayani bayan ganawar da aka yi da shi a Aso Rock, Rabiu Kwankwaso ya ce shugaban kasa ya yi mamakin jin irin ta’asar da aka yi a jihar Kano.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jawabin Rabiu Musa Kwankwaso
"Shugaban kasa ya yi mamaki. Ba za ka yi mamaki mutum ya saida jami’a ba Ba za ka yi mamaki mutum ya ruguza jami’a tilo da ake da ita ba?
Mutane wadanda su ka san Daula, ta na cikin manya-manyan gine-gine a kasar nan a lokacin Audu Bako, ya zo ya cire ta gaba daya, ya kori yaran da malaman.
Ya (Abdullahi Umar Ganduje) ya ruguza wannan. Shin ba za ku yi mamaki ba. Shugaban kasa ya yi mamaki, bai sani ba
Kamar yadda tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya ya fada, tun farko Abba Kabir Yusuf ya yi alkawari idan ya karbi gwamnati, zai gyara barnar filayen da aka yi.
‘Dan siyasar ya zargi tsohon Gwamnan da saida wadannan filaye da gine-ginen gwamnati ga ‘ya ‘yansa, ya ce hakan bai dace ba kuma ya kamata ayi gyara.
Yanzu-Yanzu: "Zan Iya Marin Kwankwaso Da Mun Hadu a Villa" Ganduje Ya Fusata da Abinda Ke Faruwa a Kano
A hirarsa, Kwankwaso ya yarda a rusa duk wata badakala da ake zargin ya yi, ya ce ko wata Gwamnati tayi ba daidai, hakan bai ba Gwamnatin Ganduje lasisi ba.
Tayin Ministan tarayya
A game da shiga gwamnatin Tinubu, Daily Trust ta rahoto tsohon ‘dan takaran shugaban kasar ya nuna bai da niyyar sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Kwankwaso yake cewa shugaba Tinubu na shirin kafa gwamnatin hadaka ne, yake cewa sun yi wannan tattaunawar, kuma zai so ya bada gudumuwarsa.
Dakatar da Gwamnan CBN
An ji labari Folashodun Adebisi Shonubi shi ne wanda zai gaji Godwin Emefiele har zuwa lokacin da za a gama bincike bayan Bola Tinubu ya dakatar da shi.
A karshen shekarar 2018 Shonubi ya zo bankin CBN, kafin nan ya yi aiki a bankuna irinsu Ecobank, Union Banki, Citi Bank da FCMB da wasu kamfanoni.
Asali: Legit.ng