Yan Sanda Sun Kwato Manyan Motoci Daga Gidan Matawalle Yayin da Suke Takun Saka da Sabon Gwamnan Zamfara
- An rahoto cewa yan sanda sun kai mamaya gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle
- Majiya ta bayyana cewa an kwato manyan motoci daga gidan tsohon gwamnan da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara
- Sabon Gwamnan Zamfara, Lawal Dare na zargin Matawalle da yin awon gaba da manyan motoci da wasu kayayyakin gwamnati
Zamfara - Rahotanni sun cewa an kwato wasu manyan motoci daga gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Majiyoyi sun fada ma Daily Trust cewa an kama manyan motocin ne yayin wata mamaya da aka kai gidan Matawalle da ke GRA a Gusau, a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni.
Sai dai kuma, jaridar ta ce bata tabbatar da adadin motocin da aka kwato ba amma wata majiya ta bayyana cewa manyan Jeep hudu aka kwace.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa jami'an yan sanda sun farmaki gidan tsohon gwamnan, wanda bai da nisa da gidan gwamnatin, Gusau.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake magana a wata tashar radiyo ta jihar, gwamnan ya ce:
"Tsohon gwamna Bello Matawalle ya tsere da motoci 17 daga ofishinsa da na ofishin mataimakin gwamna yana ikirarin cewa motocin nasa ne na kansa. Hatta ga kayan ofis basu tsira ba."
Martanin yan sanda
Ba a samu jin ta bakin ASP Yazdi Abubakar, jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Zamfara ba domin bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.
Hakazalika, ba a samu mai ba tsohon gwamnan shawara kan harkokin jama'a, Zailani Bappa ba. domin wayarsa a kashe take.
Idan za ku tuna, Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya zargi Matawalle da barin mulki da motocin gwamnati 17 da kuma sace kayayyaki ciki harda talbijin da tukunyar gas daga gidan gwamnati.
Gwamna Lawal ya ba Matawalle wa'adin kwanaki 5 ya dawo da motocin gwamnatin Zamfara da ya sace
A wani labarin kuma, Dauda Lawal, sabon gwamnan jihar Zamfara, ya ba magabacinsa, Bello Matawalle wa'adin kwanaki biyar domin ya dawo da motocin gwamnati da jami'ansa suka yi awon gaba da su yayin da yake a matsayin gwamnan jihar.
Lawal, wanda ya kasance zababben gwamna karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayar da wa'adin ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya saki.
Asali: Legit.ng