Tsohon Gwamna Ya Bar Ni Babu Motar Zuwa Ofis Ko 1 In Ji Gwamnan APC Da Ya Hau Mulki

Tsohon Gwamna Ya Bar Ni Babu Motar Zuwa Ofis Ko 1 In Ji Gwamnan APC Da Ya Hau Mulki

  • Hyacinth Alia ya maidawa jam’iyyar PDP martani a dalilin sukar shi da tayi bayan ya dare mulki
  • Gwamnan jihar Benuwai ya ce Samuel Ortom ya bar masa bashin albashi da kuma fanshon ma’aikata
  • Alia yake cewa duk da haka babu abin da yake baitul-mali sai bashin kudi, kuma ko mota bai daga ba

Benue – Mai girma Gwamna Hyacinth Alia ya koka kan abin da ya kira satar hauka da aka yi a gidan gwamnatin jihar Benuwai da ke garin Makurdi.

Punch ta rahoto Rabaren Hyacinth Alia ya na cewa gwamnatin Samuel Ortom da ta shude, ta kwashe kayayyi, har ta kai an bar shi bai da motar ofis.

Da yake bayanin halin da yake ciki, Gwamna Alia ya ce babu abin da ya gada a baitul-mali sai bashin Naira biliyan 187.56 da kuma hakkokin ma’aikata.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Daga Hawa Mulki, Gwamnan Arewa Ya Kori Ma'aikata Daga Aiki

Gwamna
Hyacinth Alia da sauran Gwamnoni a Aso Rock Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

A jawabin da ya fitar ta ofishin Babban sakataren yada labarai, Gwamnan ya ce Ortom ya bar bashin albashin ma’aikata da fanshon wadanda suka yi ritaya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tersoo Kula ya fitar da jawabin ne a matsayin martani ga jam’iyyar PDP ta reshen Benuwai da ke sukar matakan da sabon Gwamnan ya dauka bayan shiga ofis.

Jawabin Tersoo Kula

"Jam’iyyar PDP ta tafka sata a gidan gwamnati har aka kai Gwamna Hyacinth Alia bai samu mota ko guda a gidan gwamnati ba.
Ziyarar da gwamna ya kai zuwa hukumomi da cibiyoyin gwamnati ya bankado mafi munin barnar da aka taba yi a tarihin Benuwai.
Jam’iyyar da ta bar asusun babu komai a jihar kuma ta karya tattalin arzikin al’umma, ita ce yau har ta ke da bakin yin suka."

- Tersoo Kula

Kara karanta wannan

Binciken Majalisa Ya Tsumbula Gwamnatin Buhari a Badakalar Naira Biliyan 910

Babu albashi da fansho

Dailypost ta ce Alia yana ganin abin da ya dace shi ne Ortom ya nemi afuwa kan albashi da fanshon ma’aikata da ya ki biya na tsawon watanni a mulkinsa.

Sakataren labaran ya ce a lokacin PDP da ke kuka, ba a biya albashin ma’aikata daga Disamban 2022 zuwa Mayun 2023, bayan albashin watanni biyar a 2017.

Haka zalika Mai girma Alia ya ce ma’aikatan kananan hukumomi su na bin bashin albashin watanni 10, rabon da a biya fansho kuwa tun a shekarar 2021.

Tinubu ya gaji N77tr

Ku na da masaniyar cewa Shugaba Bola Tinubu ya gaji bashin Naira Tiriliyan 77 a hannun Gwamnatin Muhammadu Buhari wanda ya yi mulki kafinsa.

An samu rahoto Jimoh Ibrahim ya fadi hanya mafi sauki da Gwamnati za ta biya bashin, ya kuma ce a daina kashe kudi wajen yakar ‘Yan Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng