Zabe Saura Kwana 5, Shugaban kasa Ya Gagara Shawo Kan Zababbun ‘Yan Majalisa

Zabe Saura Kwana 5, Shugaban kasa Ya Gagara Shawo Kan Zababbun ‘Yan Majalisa

  • Ahmad Idris Wase da Abdulaziz Yari ba su sallama takarar da suke yi a zaben majalisa ba
  • Shugaban kasa ya hadu da zababbun ‘yan majalisa, amma da alama hakarsa bata cin ma ruwa ba
  • Yari da Wase ba su halarci taron da aka yi da Bola Tinubu ba, hakan ya nuna ba za su fasa takara ba

Abuja - Kwanaki biyar rak su ka rage ayi zaben shugabannin majalisar tarayya, Punch ta ce har yanzu Bola Tinubu bai samu yadda yake so ba.

Sabon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai iya dinke barakar da ta kunno kai a jam’iyyar APC ba, an samu sabanin ne a wajen yin kason kujeru.

Wata majiya ta ce a lissafin shugabancin majalisar wakilai da ake yi, ba a maganar Ahmad Idris Wase wanda ya fito ne daga Arewa maso tsakiya.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Wasu ‘Yan G7 Sun Ki Zuwa Taron da Bola Tinubu Ya Kira

Yan Majalisa
'Yan majalisa sun je Aso Rock Horo: @Buhari Sallau
Asali: Facebook

Ina labarin Hon. Ahmad Wase?

Majiyar ta ce jam’iyyar APC da shugaban kasa sun ware kujerar majalisar wakilai ne ga mutanen Arewa maso yamma, Wase kuwa mutumin Filato ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A karshe takarar da za ayi za ta kasance tsakanin Aminu Sani Jaji, Sada Soli da Tajuddeen Abbas wadanda ke wakiltar Zamfara, Katsina da Kaduna.

Rahoton ya ce Hon. Aminu Sani Jaji bai janye takararsa ba, zai kara da Tajuddeen Abbas wanda yake da goyon bayan APC da fadar shugaban kasa.

'Dan takaran G7 zai fito

A ranar Asabar ne kuma ‘Yan G7 za su yi zama domin tsaida wanda za su marawa baya ya zama ‘yan takaransu da za su gwabza da Abbas/Kalu.

Wani zababben ‘dan majalisar wakilai a PDP ya ce Bola Tinubu ya roke su da su ba jam’iyyar APC hadin-kai, ganin cewa lokacin siyasa ya wuce.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Mambobi 67 Na Bayan Yari, Abdul Ningi Ya Ce Dole a Bar ’Yan Majalisa Su Zabi Son Ransu

Kyau #3 ya zama Kirista

A zaben majalisar dattawa, Sanata Kashim Shettima ya nunawa zababbun Sanatoci muhimmancin kirista ya zama shugaban majalisa a wannan karo.

Ganin shi da shugaban kasa duk musulmai ne, Shettima ya na so ‘yan majalisa su hada-kai, su marawa Godswill Akpabio baya kan Abdulaziz Yari.

Kalu da Izunaso su na takara

Kehinde Olaosebikan wanda yake magana da yawun Osita Izunaso ya ce har gobe zababben Sanatan yana takara musamman ganin shi ma kirista ne.

Da aka tutubi Emeka Nwala a matsayinsa na Sakataren yada labaran Orji Uzor Kalu, ya ce har yanzu Sanatan Abia ta Arewa ya na neman takara a APC.

Rikicin Majalisar Nasarawa

An ji labari 'yan takara uku su ka nemi shugabancin majalisa a Nasarawa, an tsaida Shugabanni biyu ne amma a karshe aka rantsar da mutum guda.

Daniel Ogah Ogazi ya hada-kai da ‘Yan PDP majalisar dokokin jihar, ya samu kuri’u 13, mutane 11 aka ce sun zabi Rt. Hon. Ibrahim Balarabe-Abdullahi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng