Shugabancin Majalisa: Wasu ‘Yan G7 Sun Ki Zuwa Taron da Bola Tinubu Ya Kira
- Bola Ahmed Tinubu ya sake yin zama da zababbun ‘yan majalisan jam’iyyar APC a fadar Aso Rock
- Shugaban kasar ya nunawa ‘yan siyasar muhimmancin hada-kai su goyi bayan duk ‘yan takaran APC
- Ba a ga keyar Hon. Ahmed Idris Wase da Hon. Aminu Jaji a taron ba, su na cikin jagororin tafiyar G7
Abuja - Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya yi zama da zababbun ‘yan majalisa da Gwamnoni da shugabannin jam’iyyar APC a kan zaben majalisa.
Daily Trust ta ce an yi taron ne a fadar shugaban kasa a Abuja a yammacin Laraba a yayin da ake shirin rantsar da sabuwar majalisar tarayya ta goma.
Muktar Betara, Yusuf Adamu Gagdi, Miriam Onuoha da Sada Soli wadanda suke neman kujerar shugabancin majalisar wakilai sun je wajen taron.
Majalisa Ta 10: Mambobi 67 Na Bayan Yari, Abdul Ningi Ya Ce Dole a Bar ’Yan Majalisa Su Zabi Son Ransu
Ina Wase da Jaji?
Abin da ya bada mamaki shi ne ba a ga sauran ‘yan takaran irinsu Ahmed Idris Wase da Aminu Sani Jaji a wajen ba duk da cewa kuwa an gayyace su.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hon. Ahmed Idris Wase shi ne ya sauka daga kujerar mataimakin shugaban majalisa kuma ya so ya nemi kujerar tare da Femi Gbajabiamila tun 2019.
Shi kuma Hon. Jaji ya dawo majalisa ne wannan karo bayan an yi shekaru hudu babu shi.
Me Tinubu ya fada masu?
A taron da aka yi, sabon shugaban kasan ya roki zababbun ‘yan majalisan su goyi bayan wadanda jam’iyyarsa ta tsaida a zabukan na mako mai zuwa.
Injiniya Sani Bala (APC, Kano) ya shaidawa jaridar cewa zaman na su ya kasance kai-tsaye ne.
‘Dan majalisar ya ce Tinubu ya fada masu abin da yake so daga gare su a majalisa ta goma, Sani Bala ya ce bayan kusan mintina 40 kowa ya kama gabansa.
Haka zalika shugaban jam’iyyar APC na kasa ya nuna abin da yake so shi ne ‘ya ‘yan jam’iyyar su hada-kai domin gwamnatin tarayya ta ji dadin aiki.
"Bola Tinubu ya fito karara ya nuna a mara baya ga Akpabio, Barau, Abbas da Kalu. Watakila hakan ba zai yi wa Ahmad Wase da Aminu Jaji dadin ji ba."
"Duk sun fada mana idan ba mu hada-kai ba, za mu iya samun rabuwar kai a majalisa wanda a karshe hakan ba zai taimaki shugaban kasa da kasa ba."
- Sani Bala
Za a sallami 'yan majalisa da N30bn
An ji labari an ware biliyoyin kudi da nufin biyan giratuti ga duk wani ‘dan majalisa da zai koma ofis ba. Za ayi hakan ne a lokacin da ake kukan kudi.
A majalisar wakilan tarayya, mutum kusan 90 kawai za su rike kujerarsu, sauran sun fadi zabe. Akwai sababbin zababbun ‘yan majalisa fiye da 230 a kasar.
Asali: Legit.ng