'Yan Sanda Sun Kulle Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Kan Rikicin Shugabanci
- Ƴan sanda a jihar Nasarawa sun garkame majalisar dokokin jihar biyo bayan rikicin shugabancin da ake yi a majalisar
- Kwamishinan ƴan sandan jihar shi ne ya bayar da umarnin domin gujewa ɓarkewar rashin bin doka da oda
- Ricikin shugabancin ya samo asali ne kan zaɓen shugaban majalisar inda aka su mutum biyu masu kansu su ne shugabannin majalisar
Jihar Nasarawa - Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta kulle majalisar jihar bayan an zaɓi shugabanni biyu akan kujerar shugabancin majalisar, rahoton The Cable ya tabbatar.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Ramhan Nansel, ya bayyana cewa umarnin kulle majalisar ya fito daga hannun kwamishinan ƴan sandan jihar, Maiyaki Mohammed-Baba, bayan tattaunawa da sauran hukumomin tsaro a jihar.

Asali: UGC
Kakakin ya bayyana cewa an ɗauke matakin ne domin kaucewa ɓarkewar rikici, cewar rahoton Aminiya.
Rikicin shugabancin ya fara ne a ranar Talata bayan zaɓaɓɓun ƴan majalisar sun rabu gida biyu inda kowane ɓangare ya zaɓi na shi shugaban.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ɓangaren yan majalisar da ke da mambobi 11 ya zaɓi tsohon kakakin majalisar, Ibrahim Abdullahi a matsayin shugaba, yayin da ɗayan ɓangaren mai mambobi 13 ya zaɓi Daniel Ogazi a matsayin shugaba.
Abdullahi ya ce shine halastaccen shugaba
Da ya ke magana kan lamarin, Abdullahi ya bayyana cewa sake zaɓensa da aka yi ya bi tsarin da ya dace da abinda kundin tsarin mulki ya tanada.
Abdullahi ya yi magana ne lokacin da ya ke duba ɓarnar da aka yi a harabar majalisar bayan ɓarkewar rikicin shugabancin.
"A lokacin rantsar da ni da mataimakina Hon. Jacob Kudu, magatakardan majalisa da mataimakinsa duk suna wajen." A cewarsa.
"Amma abin takaici wasu sun kutsa cikin majalisa a ƙarƙashin jagorancin wani jami'i wanda ya ke a mataki na takwas, sun yi rantsuwar kama aiki."

Kara karanta wannan
Sati Daya Da Hawa Mulki, An Taso Gwamnan APC a Gaba Sai Ya Yi Murabus, An Bayyana Kwararan Dalilai
"A wajena har yanzu su zaɓaɓɓun ƴan majalisa ne saboda rantsar da su bai bi ƙa'ida ba kuma ya saɓawa tanadin tsarin doka ba."
Ya bayyana cewa duk wani bikin rantsar da zaɓaɓɓun ƴan majalisa wanda ba magatakarda ya yi shi ba, to ba ingantacce ba ne.
Matasa Sun Yi Zanga-Zanga a Harabar Majalisa
A wani rahoton na daban kuma, wasu fusatattun matasa sun gudanar da zanga-zanga a harabar majalisar dokokin jihar Nasarawa.
Matasan na zanga-zangar ne bayan an ɗage rantsar da sabbin ƴan majalisar dokokin jihar.
Asali: Legit.ng