Masari, Faleke Da Mutum 20 Da Za Su Iya Shiga Cikin Hadiman Da Tinubu Zai Nada

Masari, Faleke Da Mutum 20 Da Za Su Iya Shiga Cikin Hadiman Da Tinubu Zai Nada

  • Bola Tinubu ya bukaci majalisar dattawa ta ba shi damar nada masu taimakawa da bada shawara
  • Ana sa ran wadanda za a nada za su kunshi masu magana da yawun bakinsa da mukarraban cikin gida
  • Jerin zai iya hadawa da masu bada shawara a kan harkokin tattalin arziki, siyasa, tsaro da sauransu

Rahoton nan ya kawo sunayen wadanda legit.ng Hausa ta ke zargin za su iya zama masu ba Shugaban kasa Bola Tinubu shawara.

1. James Faleke

Akwai yiwuwar Sakataren APC PCC, Hon. James Faleke ya samu matsayin Hadimi musamman ganin bai cikin wadanda za su nemi takarar Gwamnan jihar Kogi.

2. Ibrahim Kabiru Masari

Ibrahim Kabiru Masari ya dade tare da Shugaba Bola Tinubu, sunan shi aka bada a INEC kafin a dauko Kashim Shettima, zai yi wahala ya rasa wata kujera a Aso Rock.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Manyan Sarakunan Kasar Nan a Villa, Sarkin Musulmi Ya Faɗi Wasu Kalamai

3. Nuhu Ribadu

Ana ta rade-radin Malam Nuhu Ribadu zai zama sabon NSA a Najeriya. Tsohon ‘dan sandan ya na tare da Tinubu tun lokacin zaben 2011 a karkashin jam’iyyar ACN.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bola Tinubu
Bola Tinubu a ofishin NSA Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

4. Ambasada Kunle Adeleke

A baya an rika yada Ambasada Kunle Adeleke aka nada a matsayin SCOP, ba abin mamaki ba ne ya zama mai kula da lokaci da duk harkokin shugaban kasa a ofis.

5. Olusegun Dada

Olusegun Dada zai iya zama mai taimakawa shugaban Najeriyan a kafofin sadarwa na zamani. Dada ya nemi kujerar shugaban matasan APC a 2022, amma ya hakura.

6. Abdulaziz Abdulaziz

Abdulaziz Abdulaziz kwararren ‘dan jarida ne da ya ajiye aikinsa domin taya Tinubu kamfe, da alama ya na cikin hadiman da ke magana da yawun shugaban kasa.

7. Dele Alake

Rahotanni sun nuna duk tafiye-tafiyen da shugaban kasar yake yi, yana tare da tsohon Kwamishinansa Dele Alake, akwai yiwuwar ya gaji Garba Shehu.

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Bullo Kan Sa Labulen Tinubu da Gwamnonin da Suka Yaki Atiku a PDP

8. Mahmud Jega

Wani da zai iya zama mai bada shawarar dabarun yada labarai shi ne Mahmud Jega. Gawurtaccen ‘dan jaridar ya na tare da shugaban kasar tun lokacin kamfe.

9. Hannatu Musawa

A cikin mata, Hannatu Musawa ta na cikin ‘yan gaba-gaba a kwamitin yakin neman zabe, ana yi wa Lauyan hasashen samun mukami a akalla a hadiman da za a nada.

10. Adebayo Olawale Edun

Wale Edun ya na da matsayi tun a wajen karbar mulki, Africa Intelligence ta ce ba zai rasa mukami a kan abin da ya shafi tattalin arziki a sabuwar gwamnatin nan ba.

11. Nosa Asemota

Nosa Asemota shi ne mai daukar hoton Mai girma Bola Tinubu, abin da ya rage kurum yanzu shi ne a tabbatar da shi a matsayin magajin Bayo Omoboriowo.

Sauran SAs da SSAs?

Daga cikin wadanda mu ke ganin su na iya zama masu bada shawara a harkokin shari’a, siyasa, harkokin majalisa, kasafin kudi da sauransu akwai:

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Wasu ‘Yan G7 Sun Ki Zuwa Taron da Bola Tinubu Ya Kira

12. Femi Falana

13. Babajimi Benson

14. Enitan Dolapo Badru

15. Ben Akabueze

16. Opeyemi Bamidele

17. Segun Osoba

Kujerar Mai bada shawara a kan tsaro

Wasu na ganin tseren NSA tsakanin tsohon ‘dan sanda, Malam Nuhu Ribadu ne da irinsu:

18. Abdulrahman Dambazau

19. Tukur Buratai

A karshe akwai:

20. Bisi Akande

Ko bai rike wani mukami a doka ba, ana tunanin Cif Bisi Akande mai shekara 84 zai zama kusa a mulki, da shi za a rika shawarwari musamman na siyasa.

Tinubu zai gyara kasa - Adaku Ogbu-Aguocha

An ji labari ‘yar takarar Sanatar Enugu a APC ta na cewa Adaku Ogbu-Aguocha ta na sa ran Shugaba Bola Tinubu zai hada-kan al’ummar kasar nan a lokacinsa.

Mako daya kenan da Bola Tinubu da Kashim Shettima su ka gaji Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo, jama'a na sauraron kamun ludayin gwamnatinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng