Gwamna Kefas Na Jihar Taraba Zai Binciki Gwamnatin Da Ya Gada
- Gwamnan jihar Taraba na jam'iyyar Peoples Democratic Party, Kefas Agbu, ya ce a shirye ya ke ya binciki gwamnatin da ya gada
- Gwamna Kefas ya bayyana cewa ba zai yi ƙasa a guiwa wajen bin ba'asi kan yadda aka tafiyar da harkokin kuɗi na jihar
- Gwamnatin gwamna Darius Ishaku da gwamna Kefas ya gada, ta bar bashin kusan N200bn a jihar, sannan ba ta kammala mafi yawan ayyuka ba
Jihar Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, a ranar Asabar ya bayyana cewa a shirye ya ke ya binciki harkokin kuɗi na gwamnan da ya gada, gwamna Darius Ishaku.
Kefas ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Jalingo, babban birnin jihar Taraba, cewar rahoton Leadersship.
Gwamnan ya ce yana nan yana nazari cikin lura kan rahoton miƙa mulkin da aka bashi na tsohuwar gwamnatin jihar, kan yadda ta yi amfani da kuɗaɗe.
Gwamnan ya bayyana cewa babu buƙatar a kafa kwamitin bincike na musamman saboda masu binciken kuɗi na jihar, na gudanar da bincike a matakin ministirin jihar, rahoton Thisday ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Za mu binciki lamuran gwamnatin da ta gabata a inda yakamata mu yi hakan, ba za mu yi ƙasa a guiwa ba wajen yin tambayoyi, mun san cewa akwai kwangiloli sannan mun san cewa wasu an ƙaddamar da su."
"Za mu yi duba kan ayyukan, gwamnati cigaba da gudana ta ke yi, duk da sai mun yi duba sosai kafin mu ci gaba da ayyukan da aka kaɗɗamar waɗanda ba a kammala ba."
Shehu Sani Ya Yi Wa APC Wankin Babban Bargo a Kaduna, Ya Bayyana Wani Bangare Na Musamman Da Jami'yyar Ta Gaza
Gwamna Kefas ya gaji bashin N200bn a jihar
Tsohon gwamman jihar, Darius Ishaku, ya tafi ya bar bashin kusan N200bn wanda gwamnatin gwamna Kefas ta gada.
Haka kuma binciken ƙwaƙwaf ya nuna cewa sama da kaso 92% na ayyukan da gwamnatin Ishaku da ta wuce ta kaɗɗamar a jihar ba a kammala su ba.
Gwamnan Zamfara Ya Bankado Badakalar N2.7bn
A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya zargi gwamnan da ya gada da yin sama da faɗi da motocin N2.79bn.
Gwamnan ya ce Matawalle bayan ya ware makuɗan kuɗaɗen domin siyo motocin, ya yi awon gaba da su kafin ya sauka mulki.
Asali: Legit.ng