Gwamna Makinde Ya Fadi Abinda Tawagar G5 Ta Tattauna da Tinubu a Villa
- Bayanan taron shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Nyesom Wike, Seyi Makinde da James Ibori ya bayyana
- Gwamna Makinde na jihar Oyo ya ce sun ziyarci shugaban ƙasa ne domin nuna goyon baya ga matakin cire tallafin man fetur
- Ya ce sabon shugaban ƙasa na buƙatar goyon bayan kowane ɗan Najeriya a wannan yanayi da ake ciki mai wahala
Abuja - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, ya bayyana abinda suka tattauna da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a fadarsa Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja.
Makinde tare da tsohon gwamnan jihar Ribas kuma jagoran G5 a PDP, Nyesom Wike, da tsohon gwamnan Delta, James Ibori, sun kaiwa Tinubu ziyara ranar Jumu'a.
The Nation ta rahoto cewa an hangi tawagar gwamnonin PDP a fadar shugaban ƙasa ranar Jumu'a, 2 ga watan Mayu, 2023 da misalin ƙarfe 4:00 na yamma.
Meyasa tawagar gwamnonin PDP suka ziyarci Tinubu?
Yayin da 'yan jarida suka tambaye shi dalilin da yasa suka gana da Tinubu, Gwamma Makinde ya ce sun kawo wannan ziyara ne domin nuna goyon baya ga sabon shugaban kasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalamansa, Makinde ya ce:
"Shi ne zai jagoranci ƙasar nan kuma yana buƙatar goyon baya daga gare mu, sannan ya kamata mu faɗa masa cewa ya fara da ƙafar dama kuma yana da goyon bayan mafi yawan jama'a."
Makinde ya yi magana kan cire tallafin man Fetur
Haka nan da aka tambaye shi ko sun tattauna kan batun cire tallafin mai, Gwamna Makinde ya ƙara da cewa:
"Eh mun tattauna kan batun kuma abu ne da ake ta cece kuce kansa a halin yanzu. Mun san cewa matakin zai wa yan Najeriya tsauri, duk da haka yana buƙatar goyon bayan kowa."
Bugu da ƙari, da aka tambaye shi kan yuwuwar sauya sheƙa zuwa APC mai mulki, gwamna Makinde ya ce ba bu wannan tunanin a gabansa yanzu.
INEC Ta Bayyana Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kaduna a Kotu
A wani labarin na daban kuma Hukumar zabe INEC ta faɗa wa Kotun Kaduna cewa Mallam Uba Sani ne sahihin wanda ya samu nasara a zaben 18 ga watan Maris.
INEC ta yi wannan bayani ne yayin martani kan karar da PDP da ɗan takararta, Isa Ashiru Kudan suka shigar suna kalubalantar nasarar Uba Sani.
Asali: Legit.ng