Shugaba Tinubu Ya Nada Tsohon Ministan Buhari Matsayin SGF
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da nadin tsohon minister Dakta George Akuma a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF
- Hakan na zuwa ne jim kadan bayan nada Kakakin Majalisar Tarayya Mr Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban fadar ma'aikatan shugaban kasa
- Shugaban na Najeriya kuma ya sanar da nada Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa, a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa
Fadar Shugaban Kasa, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a ranar Juma'a, 2 ga watan Yuni, ya sanar da nadin tsohon Ministan Ayyuka Na Musamman, Dakta George Akume, a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Tsohon gwamnan na jihar Benue ya yi aiki a karkashin gwamnatin Shugaba Kasa Muhammadu Buhari a matsayin ministan ayyuka na musamman.
An tabbatar da nadin Dakta George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya (SGF)
Tsohon hadimin Shugaba Muhammadu Buhari, Tolu Ogunlesi, ne ya sanar da hakan cikin wata sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sakon da Legit.ng Hausa ta gani ya ce:
"PBAT ya yi nade-nadensa na farko:
"Shugaban Fadar Ma'aikatan Shugaban Kasa, @femigbaja
"Mataimakin Shugaba Fadar Ma'aikatan Shugaban Kasa: Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa
"Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF): Tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, George Akume.
"A al'adar Najeriya, Mataimakin Shugaban Fadar Shugaban Kasa yana yi wa mataimakin shugaban kasa aiki ne."
Muhimman Abubuwa 7 Da Ya Dace Ku Sani Game Da Ministan Buhari Da Tinubu Ya Nada SGF
A yau Juma'a 2 ga watan Yuni ne Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da nadin Sanata George Akume, tsohon ministan harkokin na musamman a gwamnatin Buhari don zama Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Dakta George Akume kuma ya taba yin gwamna a jihar Benue a 1999 inda ya yi mulki na wa'adi guda biyu a jihar da ke arewacin Najeriya.
Bayan ya kammala wa'adinsa a matsayin gwamna a shekarar 2007, Akume ya yi takarar sanatan Arewa maso yammacin Benue, inda daga bisani ya zama shugaban masu rinjaye a majalisar a wani lokaci.
Baya gaza zarcewa a majalisa a 2019 ne Shugaba Buhari ya nada shi ministan ayyuka na musamman.
Asali: Legit.ng