Babban Abokin Faɗan Tinubu Ya Ajiye Kayan Yaƙi, Ya Shirya Zai Karɓi Tayin Kujera
- Olabode George ya ajiye rigar kiyayya da Bola Ahmad Tinubu, ya ce bai rigima da sabon shugaban Najeriya
- A wata hira da dattijon ya yi da manema labarai, ya nuna zai iya karbar mukami a gwamnatin APC mai-ci
- An yi shekara da shekaru ana rigima tsakanin jagora a PDP, Bode George da tsohon Gwamnan jihar Legas
Lagos - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Olabode George ya ce hankali kwance zai taimakawa gwamnatin Bola Tinubu.
Leadership ta rahoto Olabode George ya na cewa zai shiga gwamnatin sabon shugaban kasar ne idan an gayyace shi, an ba shi wani mukami.
George wanda ya dade yana rigima da tsohon gwamnan na Legas ya sauko daga kujerar da yake, ya ce zai iya bada gudumuwarsa a cigaban kasa.
Da ‘yan jarida suka yi hira da shi a ofishinsa da a Ikoyi a jihar Legas, babban jigon na jam’iyyar PDP ya nuna babu sabani tsakaninsa da Bola Tinubu.
Jita-Jita: Shin Tinubu Ya Nada Pat Utomi, Aminin Peter Obi Minista? Jigon Jam'iyyar Labour Ya Mai da Martani
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Dattijon ya ce horon da ya samu a aikin soja ba zai bar shi ya ki taimakawa kasarsa idan an ga bukatar ya taka rawar gani a gwamnatin Tinubu ba.
"Ni Soja ne" - George
Kamar yadda na fada, babu wani sabani na tsakanin mutum da mutum. Kai, a gidan soja aka horas da ni, kuma a aikin soja duk da na kusa da kai, ‘danuwanka ne.
Idan ka fita wani aiki a gidan soja, saboda a kare kasa ne. Idan ya zo ya ce mu yi aiki tare saboda kishin kasa, me zai hana ni karba? Ni ma Kasar nan tayi mani horo.
Gidan soja ya horar da ni. Babu wani bangare na Duniyar nan da ban je na samu horo, nayi atisaye ba. Kasar nan tayi mana horo.
Ya zama dole mu yi abin da zai yi tasiri ga kanana masu tasowa, mu sa su murna.
- Bode George
Rikicin gidan PDP
Da aka tambaye shi kan zaben 2023, Blueprint ta rahoto George yana cewa jam’iyyarsu ta PDP ta kunyata ne saboda tayi watsi da wasu bangarori.
A cewar ‘dan siyasar, an maida yankinsa na Kudu maso yamma saniyar ware a PDP, da suka yi magana sai aka ce su jira tukuna, a karshe aka fadi zaben.
Nadin mukamai a gwamnati
Jita-jita sun cika gari cewa Femi Gbajabiamila ne sabon Shugaban Ma’aikatan fadar Gwamnati, mun bi diddikin lamarin har mun kawo maku rahoto a kai.
Hadimin Shugaban majalisar wakilan kasar, Olanrewaju Smart Wasiu ya fayyace gaskiyar batun, ya ce Bola Tinubu bai ba mai gidansa wani mukami ba.
Asali: Legit.ng