Shehu Sani Ya Yi Wa El-Rufai Tonon Silili, Ya Bayyana Abinda Ya Ke Jiran Samu Daga Wajen Shugaba Tinubu

Shehu Sani Ya Yi Wa El-Rufai Tonon Silili, Ya Bayyana Abinda Ya Ke Jiran Samu Daga Wajen Shugaba Tinubu

  • Shehu Sani ya ƙalubalanci tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyanawa duniya kadarorinsa
  • Tsohon sanatan ya yi zargin cewa El-Rufai yana jiran samun wani muƙami mai gwaɓi daga wajan shugaba Tinubu, bayan ya yi wa Amaechi aiki
  • A cewar Sani, El-Rufai ya bar ɗumbin bashi ga al'ummar jihar Kaduna bayan ya miƙa mulki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu

Jihar Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu ya ƙalubalanci tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da ya bayyana kadarorin da ya mallaka.

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa El-Rufai yana jiran samun muƙami daga wajen shugaba Tinubu bayan kuma tsohon gwamnan jihar Rivers ya yi wa aiki.

Shehu Sani ya kalubalanci El-Rufai
Shehu Sani da El-Rufai Hoto: Nasir El-Rufai/Shehu Sani
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter @ShehuSani a ranar Laraba, lokacin da ya ke martani kan iƙirarin da El-Rufai ya yi na cewa bai saci ko sisin kwabo ba na jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Ya Taki Sa'a: Babban Hadimin Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Samu Aiki Mai Gwaɓi Bayan Karewar Mulki

Tsohon sanatan ya yi zargin cewa, El-Rufai ya tafi ya bar mutanen jihar Kaduna da biyan ɗumbin bashi, bayan ya bar ofis a ranar 29 ga watan Mayu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Mr Elrufai, tsohon gwamna mai ritaya ya koma watsa labarai a Twitter, yayin da ya ke jiran muƙami daga wajen Tinubu, bayan ya yi wa Amaechi aiki da yaɗa labarai marasa kyau ta ƙarƙashin ƙasa."
"Ka bar ɗumbin bashi ga ƴaƴanmu da jikokinmu su biya a jihar Kaduna, sannan ka yi iƙirarin ba ka taɓa satar ko sisi daga asusun jihar Kaduna ba. Ɗaya daga cikin ƴan barandarka har cewa ya yi arziƙin ka ma raguwa ya yi."
"Idan ka isa ka bayyana kadarorin ka ta hanyar nunawa duniya fom ɗin da miƙawa hukumar ɗa'ar ma'aikata, daga na shekarar 2015 har na 2023. Zan yi maka martani idan ka yi hakan."

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Tattara Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP, Gaskiya Ta Bayyana Daga Mamban NEC

Ɗan El-Rufai ya yi martani bayan Shehu Sani ya ƙalubalanci mahaifinsa

Bashir, ɗaya daga cikin ƴaƴan El-Rufai ya yi martani kan ƙalubalantar da Shehu Sani ya yi wa mahaifinsa. Ya bayyana cewa tsohon Sanata ya ƙyale mahaifinsa daga takalar faɗa a Twitter, ya koma kan ƴaƴansa domin su ne sa'annin yin sa.

A kalamansa:

"Saboda Allah haka kake yi wa na gaba da kai magana? Ka kyale takalar faɗa a Twitter tsakanin ka da mu ƴaƴansa. Mu ne abokan yin ka."

Uba Sani Ya Bayyana Makomar Ayyukan Da El-Rufai Bai Kammala Ba a Kaduna

A wani rahoton na daban kuma, gwamnan jihar Kaduna, sanata Uba Sani ya baƴyana cewa zai kammala ayyukan da El-Rufai ya fara bai kammala ba a jihar.

Sabon gwamnna ya bayyana cewa kafin ya fara aiwatar da ayyukansa, sai ya kammala na tsohon gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng