"Zan Kammala Dukkanin Ayyukan Da El-Rufai Ya Fara a Kaduna", Uba Sani

"Zan Kammala Dukkanin Ayyukan Da El-Rufai Ya Fara a Kaduna", Uba Sani

  • Gwamna mai jiran gado na jihar Kaduna ya yi alƙawarin kammala dukkanin ayyukan da gwamna El-Rufai ya fara a jihar
  • Sanata Uba Sani ya sha wannan alwashin ne bayan ya karɓi rahoton kwamitin miƙa mulki a hannun gwamna El-Rufai
  • Uba Sani ya bayyana cewa kafin ya fara aiwatar da sabbin ayyuka a jihar, sai kammala ayyukan da El-Rufai ya ɗauko a jihar

Jihar Kaduna - A yayin da ake tunkarar ranar 29 ga watan Mayun 2023, zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kaduna, sanata Uba Sani, ya yi alƙawarin kammala ayyukan da gwamna mai barin gado na jihar ya fara, kafin ya fara gudanar da sabbin ayyuka.

Uba Sani ya bayyana hakan ne bayan gwamna mai barin gado, Nasir Ahmed El-Rufai, ya miƙa masa rahoton kwamitin karɓar mulki a gidan gwamnatin jihar Kaduna na Sir Kashim Ibrahim a birnin Kaduna, rahoton Leadership ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Nada Sabon Kwamishina Yana Dab Da Sauka Kan Mulki

Uba Sani ya yi alƙawarin kammala ayyukan El-Rufai a Kaduna
Gwamna El-Rufai ya mika rahoton kwamitin mika mulki ga Uba Sani. Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A yayin da ya ke yabawa gwamnan mai barin gado, ya bayyana cewa zai yi duba kan rahoton sannan zai aiwatar da shawarwarin da aka bayar a cikinsa, cewar rahoton The Cable.

A kalamansa:

"Ina son miƙa godiyata ga shugabana kuma ubangidana, gwamna Nasir El-Rufai. A tare da shi mun zaɓi mutanen da suka samar da rahoton kwamitin miƙa mulki. Zan yi duba kan rahoton sannan za mu aiwatar da mafi yawan shawarwarin da ya bayar."
"A shekarar 2015, ba mu samu irin wannan damar ba. Za mu kammala dukkanin abubuwan da gwamna El-Rufai ya fara sannan za mu yi aiki akan wasu sabbin ɓangarori."

El-Rufai ya miƙa rahoton kwamitin miƙa mulki ga Uba Sani

Tun da farko, gwamna mai barin gado na jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya miƙa rahoton kwamitin miƙa mulki ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar, sanata Uba Sani.

Kara karanta wannan

Zababben Gwamnan Kano, Abba Gida-Gida Ya Bayyana Kadarorinsa Gabanin Rantsar Da Shi

Da ya ke magana yayin gabatar da rahoton, El-Rufai ya yabawa kwamitin miƙa mulkin, inda ya bayyana cewa rahoton zai zama wata mahanga ga gwamnati mai jiran gado ta magajinsa.

El-Rufai ya yi nuni da cewa a shekarar 2015 bayan ya tiƙa abokin hamayyarsa da ƙasa ya lashe zaɓen gwamnan jihar, ba a ba shi rahoton miƙa mulki ba, sai dai shi da tawagarsa suka zauna suka samar da na su, wanda ya yi aiki da shi.

Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Dalilin Gayyato Kwankwaso Zuwa Jihar

Rahoto ya zo kan yadda gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya gayyato madugun Kwankwasiyya, sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin buɗe wasu ayyuka a jihar.

Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa ya yi hakan ne saboda kamfanin wani yaron Kwankwaso ne ya yi aikin kwangilar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel