Shugaba Tinubu da Shettima Sun Yi Muhimman Naɗe-Naɗe Biyu

Shugaba Tinubu da Shettima Sun Yi Muhimman Naɗe-Naɗe Biyu

  • Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya naɗa Nosa Semota a matsayin mai ɗaukar hotonsa a hukumance tsawon zangon mulkinsa
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi makamancin wannan naɗin inda ya ɗauki Ope Adelani
  • Wannan naɗin ya fito ne daga bakunan tsoffin masu ɗaukar hoton tsohon shugaba Buhari da mataimakinsa

FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Nosa Semota a matsayin mai ɗaukar hotonsa na kai da kai awanni bayan shiga Ofis a karon farko.

A ɗaya bangaren an naɗa Ope Adelani a matsayin mai ɗaukar hoton ofishin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, yayin da suka fara zangon mulki na tsawon shekara huɗu.

Hoton hadaka.
Shugaba Tinubu da Shettima Sun Yi Muhimman Naɗe-Naɗe Biyu Hoto: Bayo Omoboriowo
Asali: Twitter

Duk da har yanzu babu sanarwa a hukumance game da naɗin Semota, amma manyan jiga-jigai masu kusanci da fadar shugaban kasa sun fara taya shi murnar samun wannan matsayi.

Kara karanta wannan

Ya Taki Sa'a: Babban Hadimin Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Samu Aiki Mai Gwaɓi Bayan Karewar Mulki

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Nosa Semota, fitaccen mai ɗaukar hoto ya jima yana wa Bola Tinubu aiki tsawon lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanene mai ɗaukar Hoton Tinubu tun da ya shiga Ofis?

Bayo Omoboriowo, tsohon mai ɗaukar hoton tsohon shugaban ƙasan da ya gabata, Muhammadu Buhari, ne ya sanar da naɗin Mista Semota kuma ya taya shi murna.

Omoboriowo ya rubuta a shafinsa na Tuwita ranar Talata 30 ga watan Mayu, 2023 cewa:

"Ku bani dama na gabatar muku da Nosa Semota (@nosasemota) a matsayin mai ɗaukar hoto a hukumance na sabon shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu."
"Wannan Sarki ne da ya cancanci mu mara masa baya, mu haɗu mu masa fatan alheri. Muna maka fatan zama cikin soyayya da zaman lafiya a ko da yaushe ɗan uwa"

Wanene mai ɗaukar hoton Shettima?

Haka zalika a ɗaya bangaren, tsohon mai ɗaukar hoton tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, Tolani Alli, ya sanar da naɗin Ope Adelani a matsayin mai ɗaukar hoton Kashim Shettima.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Shiga Villa a Karon Farko, Zai Yi Nade-Nade Masu Muhimmanci

Ya taya shi murna a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, inda ya ce:

"Ina taya ku murna, Neso Semota, mai ɗaukar Hoton Bola Tinubu da Ope Adelani (@opeadelani) a matsayin mai ɗaukar hoton Ƙashim Shettima."
"Ina muku fatan samun nasara, tsaro da kariyar Allah a sabon matsayin da kuka taka, Allah ya muku albarka."

Tsohon Gwamnan Ribas, Wike Ya Jima da Barin Jam'iyyar PDP, Inji Mamban NEC

A wani labarin na daban kuma Jigon PDP na kasa ya bayyana cewa tuni suka ɗauki tsohon gwamna Ribas, Wike a matsayin wanda ya fice daga jam'iyyar.

Ya ce Nyesom Wike ya jima da rasa martabarsa a inuwar PDP kuma shi kansa idan zai faɗi gaskiya ya san ba ɗan jam'iyya bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262