Duniya Juyi-Juyi: Yadda Na Tashi Ranar Farko a Matsayin Tsohon Gwamna Inji El-Rufai

Duniya Juyi-Juyi: Yadda Na Tashi Ranar Farko a Matsayin Tsohon Gwamna Inji El-Rufai

  • Mulki ya kare bayan shekaru takwas, rayuwar Nasir Ahmad El-Rufai ta zama kamar kowane talaka
  • Tsohon Gwamnan ya yi wani rubutu mai jan hankali, ya na kira ga matasa da manya a shafin Twitter
  • El-Rufai ya nuna ya rabu da wahalhalun shugabanci, amma ya bukaci matasa su bada gudumuwarsu

Abuja - Nasir Ahmad El-Rufai ya yi wani gajeren rubutu a shafinsa na Twitter, ya na magana a game da rayuwa bayan sauka daga mukami.

Nasir Ahmad El-Rufai ya ce jiya ta kasance ranar da ta fi masa sauki a kusan shekaru goma, domin ya rabu da hayaniyar mulki da gwamnati.

Malam El-Rufai wanda ya rike Sakataren APC na kasa kafin ya zama Gwamnan jihar Kaduna a 2015, bai da nauyin al’umma yanzu a kan shi.

Gwamna El-Rufai
Nasir El-Rufai kafin ya bar ofis Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Tsohon Ministan babban birnin tarayya ya yi kira ga matasa su shirya yin amfani da karfinsu wajen ba gwamnati gudumuwa idan an ba su mukami.

Kara karanta wannan

Miji Ya Je 'Hotel' Holewa da Budurwarsa, Ya Yi Cikibus da Matarsa, Ya Ga Abinda Ya Ɗaga Masa Hankali

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Su kuwa dattawa, da yake magana a shafinsa, El-Rufai ya ce su yi amfani da ganin jiya da yau da su ka yi wajen tasa matasa gaba domin ayi nasara.

Jawabin Nasir El-Rufai

"Babu kiran waya ko a buga mani kofar daki ko Adejoh Momoh ya tattaro mani jerin ayyuka, ko in yi ta shiga nan da can domin cin ma lokaci, ko kuwa karanta rahoton tsaro da wuri domin a ce in fitar da umarni!
"Saboda haka ga mutane da-dama iri na, rayuwa ta fi sauki – amma ga matasan zamaninmu, ku san cewa ba ku da damar kauracewa siyasa da shugabancin al’umma.
"Ku shirya sadaukar da lokacinku da arzikinku domin taimakawa shugaban kasa Asiwaju (Bola Tinubu) da duka Gwamnonin jihohinku da zarar an neme ku.
"Ga manya masu yawan shekaru, sanin aiki, wadata da daraja, ‘yan kadan daga cikinku su shirya bautawa kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu: Muhimman Abubuwa 7 da Aka Tsakura Daga Jawabin Sabon Shugaban Kasa

"Ku shirya bada gudumuwar ilmi, basira da tunaninku wajen zaburar da matasa su iya shawo kan matsalolin kasarmu.
"Ta haka ne za mu yi aiki tare domin mu iya samun Najeriyar da shugaba Tinubu ya ce ya ke so a jawabin rantsuwarsa."

- @elrufai

Ina Muhammad Sanusi II?

Ku da labari Muhammad Sanusi II ya je bikin rantsar da sabon Gwamnan jihar Abia, Alex Otti wanda sun yi aiki tare da shi a banki a shekarun baya.

‘Dan Buram na Kano, Munir Sanusi Bayero ya wakilci Khalifa Sanusi II wajen rantsar da Abba Kabir Yusuf a matsayin sabon Gwamnan jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng