Sanusi Ya Ki Amsa Gayattar Abba, Ya Je Bikin Rantsar da Abokinsa da Ya Zama Gwamna
- Kowa ya san ba a ga maciji yanzu tsakanin Rotimi Amaechi da magajinsa, Nyesom Wike a Ribas
- Tsohon Ministan bai halarci wajen rantsar da sabon Gwamnan Ribas ba, kuma bai je Eagle Square ba
- Shi ma Muhammadu Sanusi II ya tafi Abia yayin da wasu ke tunanin za a gan shi a jiharsa ta Kano
Abia - A maimakon a hange shi tare da baki masu alfarma a filin Eagle Square, sai aka ga Rotimi Amaechi wajen rantsar da Gwamna a Umuahi a jihar Abia.
Leadership ta ce tsohon Ministan sufuri kuma jigo a jam’iyyar APC, Rotimi Amaechi bai halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba.
A ranar Litinin, tsohon Gwamnan na Ribas ya na filin wasan Umuahia inda aka rantsar da Alex Otti a matsayin sabon Gwamnan jihar Abia a karkashin LP.
Ba ‘dan siyasar kadai ne fitaccen mutumin da ya halarci bikin rantsar da Dr. Alex Otti a Abia ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanusi II da Alex Otti
Rahoton gidan talabijin Channels ya tabbatar da cewa Mai martaba Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sanusi II ya na cikin wadanda suka ci taron ranar.
Wata majiya ta ce Sanusi II ya yi aiki da Otti a bankin First Bank, sannan amininsa ne har bayan lokacin da ya bar bankin, ya rike shugabancin Diamond Bank.
Wasu sun yi tunanin Khalifan na Tijjaniya zai halarci bikin rantsar da sabon Gwamnan Kano inda Mai girma Abba Kabir Yusuf ya aiko masa da gayyata.
Munir Sanusi Bayero wanda shi ne 'Dan Buram na Kano ya wakilci Khalifa. .
Bayan rantsar da sabon shugaban kasa da aka yi a Abuja, akwai jihohi 28 da aka rantsar da sababbin Gwamnoni ko Gwamnoninsu suka shiga wa’adi na biyu.
Sauran baki a Abia
Yayin da kusan duk wasu manya da ake ji da su na Abuja, jihar Abia ta ga bakuncin irinsu shugaban jam’iyyar LP, Julius Abure da Datti Baba-Ahmed.
‘Dan takaran mataimakin shugaban kasa a LP a zaben 2023 ya halarci rantsuwar Otti a Abia.
Rahoto ya ce sauran manyan baki na musamman sun hada da tsohon Gwamna, Sanata Theodore Orji da Sanatan Abia ta Kudu, Enyinnaya Abaribe.
An hana Ganduje shiga VIP
Labari ya zo cewa ba a kyale Dr. Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Hafsah Ganduje zama tare da baki masu alfarma wajen rantsar da Bola Tinubu ba.
Tsohon Gwamnan na Kano bai da takardar gayyatar da zai shiga sashen manyan baki, don haka dolensa ya zauna da sauran jama'a a wata rumfa.
Asali: Legit.ng