Bidiyo: Kalli Lokacin Da Buhari Ya Tashi Zuwa Gida Daura Bayan Mika Mulki Ga Tinubu
- Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mikragamar harkokin kasar ga sabon shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
- Bayan mika mulki ga Tinubu, Buhari da matarsa, Aisha sun bar Abuja sannan daga nan suka shiga jirgin saman sojin Najeriya mai lamba 001 zuwa Katsina a hanyarsu ta zuwa Daura=
- Bayan ya yi musabaha da gaisawa da wasun su, Buhari ya daga hannu don bankwana da hadimansa kafin jirgin ya tashi
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da matarsa, Aisha sun bar babban birnin tarayyar kasar, Abuja, bayan mika mulki ga magajinsa, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023.
Buhari da matarsa sun samu rakiyar wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatinsa zuwa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja.
Buhari ya tafi Daura
Tsohon shugaban kasar Najeriya ya bar Eagle Square, Abuja, bayan mika mulki ga shugaban kasar Najeriyana 16, sannan daga nan ya hau jirgin saman sojin Najeriya mai lamba 001 zuwa Katsina a hanyarsa ta zuwa mahaifarsa Daura.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bidiyon Buhari yayin da ya tafi mahaifarsa Daura bayan mika mulki ga Tinubu
Wani bidiyo mai tsuma zuciya da Bahir Ahmad ya wallafa a Twitter ya nuno lokacin da tsohon shugaban kasar ya shiga jirgi da yin bankwana ga mambobin majalisarsa.
Kalli bidiyon a kasa:
Na matsu na ga Shanu na sun fi saukin juyawa akan ’yan Najeriya, Buhari
A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya matsu ya koma gida Daura da ke jihar Katsina bayan ya gama mulkinsa a yau Litinin 29 ga watan Mayu.
Buhari ya bayyana haka ne a yayin taron cin abinci da aka gudanar a ranar Lahadi 28 ga watan Mayu a babban birnin tarayya Abuja.
A cewar Buhari, ya kosa sosai ya koma mahaifarsa ta Daura da ke jihar Katsina saboda ya ci gaba da kula da shanunsa wadanda suka fi masa saukin juyawa sosai akan ‘yan Najeriya.
Jaridar Thisday ta rahoto Buhari yana cewa:
“Na zaku gobe ta zo na koma gida don nakula da shanu da tumaki na saboda sun fi smani aukin juyawa akan ‘yan uwana ‘yan Najeriya.”
Asali: Legit.ng