Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game da Sabon Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda
- A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu ne aka rantsar da zababben gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda da mataimakinsa Faruk Lawal Jobe a kan karagar mulki
- Dikko Radda zai gaji gwamna mai barin gado, Aminu Bello Masari, wanda ya shafe shekaru takwas yana mulkar jihar ta Katsina
- Manyan baki daga sassa daban-daban na ciki da wajen jihar ta Katsina, sun halarci bikin rantsuwar da ya gudana a filin wasa na Dikko Stadium da ke Katsina
Katsina - An rantsar da dakta Dikko Umar Radda a matsayin gwamnan jihar Katsina ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke cikin birnin Katsina.
Dikko shi ne wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Katsina da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris, shekara ta 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulki kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Dikko, ɗan shekara 52, shi ne tsohon darakta janar na hukumar bayar da tallafi ga ƙanana da matsakaitan masana'antu ta ƙasa (SMEDAN).
Taƙaitaccen tarihin Dikko Radda
An haifi Dikko Radda a ranar 10 ga watan Satumban shekarar 1969, a garin Hayingada da a wancan lokacin ke a ƙaramar hukumar Dutsinma a jihar Katsina.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya yi makarantar firamare a makarantar firamare ta garin Radda daga 1974 zuwa 1980.
Daga nan Dikko ya wuce zuwa makarantar horas da malamai da ke Zaria, wacce ya kammala a shekarar 1985.
Kamar yadda aka wallafa a shafin cibiyar kasuwanci ta duniya GEN, Dikko ya yi karatun NCE a makarantar ilimi ta Kafancan jihar Kaduna, daga 1986 zuwa 1989.
Daga nan kuma sai ya wuce jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi a shekarar 1992.
Dikko ya kammala karatunsa na digiri a ɓangaren tattalin arziƙin noman zamani a shekarar 1996.
A shekarar 1998, Dikko Radda ya ci-gaba da karatun digiri na biyu a ɓangaren noma a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, wanda ya kammala a shekarar 2004.
Ya kuma ƙara yin wani masta digiri a ɓangaren harkokin huldoɗin ƙasashen waje a ABU a shekarar 2005.
Dikko Radda ya sake komawa jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda ya yi digirinsa na uku a ɓangaren harkokin noma da ya kammala a shekarar 2015.
Ya yi ayyuka da dama a can baya da suka haɗa da koyarwa da kuma aikin banki. Sannan Dikko ya riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Charanchi na tsawon shekaru biyu, wato daga 2005 zuwa 2007.
Dikko ya kuma riƙe shugaban ma'aikata na gwamnatin tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a zagayen farko.
Kalubalen da ya fuskanta dangane da nasararsa
A baya dai, babban abokin hamayyar Dikko a zaɓen gwamnan jihar ta Katsina da ya gabata, Sanata Yakubu Lado Danmarke na jam’iyyar PDP, ya yi barazanar garzayawa kotu domin kalubalantar sakamakon zaɓen.
Sai dai daga bisani Yakubu ya fasa shigar da ƙarar a kotu, wanda hakan ke nuna cewa Dikkon zai ci gajiyar wa’adin mulkinsa na farko ba tare da wani kalubale ba.
Dikko da mataimakinsa Faruk Lawal Jobe, sun yi rantsuwar kama aiki a gaban babban alƙalin jihar Katsina, Danladi Abubakar, a tsakanin karfe 10:40 zuwa 10:45 na safe kamar yadda ya zo a rahoton The Punch.
Faruk Lawal Jobe shi ne tsohon kwamishinan kuɗi na jihar Katsina a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Aminu Bello Masari.
An yi wa sarkin Kano, Aminu Ado ihu a wajen rantsar da Abba Gida-Gida
A wani labarin kuma, wasu daga cikin magoya bayan sabon gwamnan Kano, injiniya Abba Kabir Yusuf, sun yi wa sarkin Kano ihu a wajen bikin rantsar da Abban da ya gudana ranar Litinin a Kano.
A cikin wani ɗan guntun bidiyo, an hango mutane sanye da jajayen huluna na yi wa sarkin na Kano ihu a lokacin da ya iso filin ƙwallon ƙafa na Sani Abacha da ke ƙofar mata.
Asali: Legit.ng