Mulki Ba Sauki: Shanu Na Sun Fi Saukin Juyawa Akan ’Yan Najeriya, Cewar Buhari
- Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya zaku ya koma gida Daura don kula da shanunsa da tumaki
- Ya ce zai koma ne ya kula da shanunsa da tumaki saboda sun fi saukin kulawa da juyawa fiye da ‘yan Najeriya
- Buhari ya bayyana haka ne a taron cin abinci a ranar Lahadi 28 ga watan Mayu tare da manyan baki
FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce ya matsu ya koma gida Daura da ke jihar Katsina bayan ya gama mulkinsa a yau Litinin 29 ga watan Mayu.
Buhari ya bayyana haka ne a yayin taron cin abinci da aka gudanar a ranar Lahadi 28 ga watan Mayu a babban birnin tarayya Abuja.
Da yake magana akan zaben wannan shekara da aka gudanar, Buhari ya taya ‘yan Najeriya murna inda ya ce yanzu ‘yan Najeriya suna da iko a hannunsu ta hanyar amfani da kuri’unsu su daura ko sauke wanda suke so.
Shugaban ya ce babban zaben da aka gudanar ya tabbatar da cewa ‘yan Najeriya su suke da akalan jagoranci, cewar Vanguard.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Buhari ya zaku ya koma Daura
Shugaba Buhari ya kara da cewa ya kosa ya koma Daura saboda ya ci gaba da kula da shanunsa wadanda suka fi saukin juyawa akan ‘yan Najeriya, cewar jaridar THISDAY.
A cewarsa:
“Na zaku gobe ta zo na koma gida don kula da shanu da tumaki saboda sun fi saukin juyawa akan ‘yan uwana ‘yan Najeriya.”
Buhari ya godewa shugabannin duniya
Buhari ya godewa shugabannin kasashe da kuma wadanda suka wakilce su don halartar wannan taro da kuma goyon baya da suka ba shi, sannan ya musu fatan alkairi.
Ya kara da cewa:
“Masu girma, shugabannin kasashe da wadanda suka wakilce su, ina muku godiya matuka kuma ina muku bankwana da kuma fatan alkairi gare ku.”
Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, da takwararsa ta Ghana, Nana Akufo-Addo da Julius Maado Bio na Saliyo duk sun samu halartar wannan gagarumin taro.
Saura Kwana 6: Na Matsu Na Gama Mulkina Saboda Matsin Lamba, Buhari Ya Koka Kan Ayyuka
A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya matsu ya gama kwana shida da suka rage saboda ayyukan da suka masa yawa.
Shugaban ya fadi haka ne a ranar Talata 23 ga watan Mayu yayin bikin cin abinci da jami'an sojin kasar su ka shirya.
Asali: Legit.ng