Jerin Sunayen Gwamnonin Da Suka Miƙa Mulki Ba Tare Da Bashin Albashin Ma'aikata a Kansu Ba

Jerin Sunayen Gwamnonin Da Suka Miƙa Mulki Ba Tare Da Bashin Albashin Ma'aikata a Kansu Ba

Wasu gwamnonin na barin ofis ba tare ƙin biyan albashin ma’aikata ba a tsawon shekaru 8 da suka yi suna mulkar al’ummar jihohinsu.

Waɗannan gwamnonin dai masu barin gado na miƙa mulki ne ga waɗanda za su gaje su bayan yi wa jihohinsu aiki na tsawon shekaru 8.

Duk da cewa akwai wasu gwamnonin da suka riƙe albashin ma’aikata kuma gashi yanzu za su bar mulki, hakan na nuni da cewa za su bar wa gwamnatocin da za su gajesu aikin biyan bashin.

Gwamnonin da suka mika mulki ba tare da kin biyan albashi ba
Sunayen gwamnonin da suka mika mulki ba tare da barin bashin ma'aikata ba. Hoto: Nasir El-Rufai, Abubakar Atiku Bagudu, Udom Emmanuel
Asali: Twitter

Yayin da wadannan gwamnonin ke barin mulki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, Legit.ng ta lissafo wasu daga cikinsu da basu bar bashi ko ɗaya na albashin ma'aikata ba.

Sai dai hakan ba wai yana nufin ba a bin gwamnonin da ke barin gadon kuɗaɗen 'yan fansho da makamantansu ba.

Kara karanta wannan

"Tallafin Man Fetur Ya Tafi," Shugaba Tinubu Ya Fara Ɗaukar Matakai Masu Tsauri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerin sunayensu mun kawo muku su a ƙasa:

Nasiru El-Rufai

Ɗaya daga cikin gwamnonin da suka miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu ba tare da barin bashin albashin ma’aikata ba, shi ne gwamnan jihar Kaduna mai barin gado, Malam Nasir El-Rufai.

Ana kallon El-Rufai a matsayin ɗaya daga cikin gwamnonin da suka taka rawar gani a tsawon shekaru 8 da ya yi yana mulki a jihar.

Abdullahi Umar Ganduje

Tsohon gwamnan jihar Kano na ɗaya daga cikin gwamnonin da suka kammala ba tare da matsalar rashin biyan albashin ma’aikata ba.

Sai dai kuma abin rashin jin daɗinsa shi ne, ɗan takararsa bai yi nasarar lashe zaɓen gwamnan da aka yi a ranar 18 ga watan Maris ba, sakamakon adawa mai zafi da gwamnatinsa ta samu a kakar zaɓen.

Okezie Ikpeazu

Gwamnan jihar Abia da ya bar ofis, na ɗaya daga cikin gwamnonin da suka bar ofis tare da barin ma’aikatan jihohinsu cikin farin ciki saboda basa binsa bashin kuɗaɗen albashi.

Kara karanta wannan

Matakalar Taron Rantsar da Abba Gida Gida Ta Rushe Yayin Bikin Rantsar da Shi a Kano

Kwanaki kaɗan gabanin barinsa ofis, Ikpeazu ya ba da umarnin a biya dukkan ma’aikatan jihar kuɗaɗensu domin yayewa kansa duk wani bashi.

Udom Emmanuel

Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom ma ya miƙa mulkin jiharsa salin alin ba tare da riƙewa ma'aikatan jihar sisin kobo ba.

Gwamnan dai shi ne shugaban yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen da ya gabata.

Abubakar Atiku Bagudu

Gwamnan jihar Kebbi bai riƙe albashin ma'aikatan jihar ba a tsawon shekaru 8 da ya shafe yana mulkin jihar da ke yankin arewa maso yamma.

Bagudu wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC, ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙin neman zaɓe da nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Gwamnoni huɗu da suka yi hanƙoron ƙaddamar da ayyuka gabanin miƙa mulki

A can baya mun kawo muku labarin wasu gwamnoni guda huɗu da suka yi faka-faka wajen ƙaddamar da ayyukan da suka gabatar a jihohinsu gabanin miƙa mulki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Abba Gida-Gida Ya Sha Alwashi Kan Gwamnatin Ganduje, Zai Yi Mata Binciken Kwakwaf

Daga cikin ayyukan da waɗannan gwamnoni suka ƙaddamar hadda wasu ma da ba a kammala ba.

Wasu daga cikinsu kuma sun sanya tushen sabbin ayyuka da nufin waɗanda za su gajesu su ƙarisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng