Tinubu: ‘Dan takaran LP, Peter Obi ya yi maganar ‘shirin’ zanga-zanga a Eagle Square

Tinubu: ‘Dan takaran LP, Peter Obi ya yi maganar ‘shirin’ zanga-zanga a Eagle Square

  • Peter Obi da mutanensa ba za su yi wata zanga-zanga a Eagle Square kamar yadda ake ta yadawa ba
  • Hadimin ‘dan takaran shugaban kasar, Tai Obasi ya tabbatar da haka ana shirin rantsar da Bola Tinubu
  • Obi mutum ne mai neman zaman lafiya, Obasi ya ce uban gidansa bai san da batun yin zanga-zanga ba

Abuja - Peter Obi ya na cikin wadanda su ka yi takara da Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2023, ya tabbatar da ba zai je bikin rantsuwar 29 ga Mayu ba.

Punch ta ce a ranar Lahadi, Tai Obasi ya fitar da jawabi a madadin ‘dan takaran, inda ya ce bai da niyyar zuwa wajen rantsar da zababben shugaban kasar.

Hakan na zuwa a lokacin da rade-radi ke yawo cewa ‘dan takaran na LP da magoya bayansa watau ‘Yan Obidient za su yi zanga-zanga a Eagle square.

Kara karanta wannan

A banza: Peter Obi ya fadi abin da zai faru dashi bayan an rantsar da Tinubu

Peter Obi
Peter Obi a Ribas Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Jita-jitar da ake yi ita ce masu adawa da Asiwaju Bola Tinubu za su je har farfajiyar rantsuwar domin su nuna rashin amannansu da sabuwar gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto Obasi ya karyata wadannan rahotanni, ya na cewa bai san daga inda su ka fito ba.

Zanga-zanga a Abuja

"Ban san daga ina rahoton nan ya ke fitowa ba. Ba mu san komai game da shi ko masu shirya wannan zanga-zanga ba.
Amma ina mai iya tabbatar maka da cewa mai gida na bai san da komai a game da wannan ba.
Shi ne Obi, mabiyansa kuma Obidient masu biyayya ne. Na yarda wasu lokutan su kan yi abubuwa a kan karon kan su.
Ko sau nawa aka nemi su yi hakuri, mutanen nan a fusace su ke. Ba su ji dadin yadda aka tafkawa Peter Obi magudi ba.

Kara karanta wannan

Mukamai 3 da Ake Sauraron Sabon Shugaban Kasa Ya Nada da Zarar Ya Shiga Ofis

Mai gidana mutum ne mai saukin kai da fahimta, wanda a kullum ya ke neman zaman lafiya da hadin-kai ko me zai faru.

- Tai Obasi

Obi zai halarci bikin rantsuwa?

"Amma zai yi wani bam-bara-kwai ya halarci bikin rantsar da mutumin da ya ke kalubalantar zaben shi a gaban kotu.
Ban san ko an aiko masa da gayyata ba. Amma ina mai fada maka cewa ba za ka gan shi a wurin ba."

- Tai Obasi

Lambar girmamawa

A gefe guda, rahoto ya zo cewa Ma’aikatar ayyuka na musamman ta fitar da sunayen tsofaffi da Gwamnoni masu-ci da za a ba shaidar girma a Najerya.

A jerin akwai shararrun 'yan siyasa da kuma Sarakunan gargajiya. Za a karrama Abdullahi Ganduje, Ali Modu Sheriff, Remi Tinubu da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng