"Arzikina Ya Ragu Sosai a Shekara Hudu", Gwamna Seyi Makinde

"Arzikina Ya Ragu Sosai a Shekara Hudu", Gwamna Seyi Makinde

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya koka kan yadda arziƙinsa ya samu koma baya a shekara huɗun da ya yi yana gwamna
  • Seyi Makinde ya ce tattalin arziƙinsa ya samu tawaya da wajen kaso 12% a shekara huɗu da ya yi yana mulkin jihar
  • Makinde ya bayyana cewa ya samu karayar arziƙin ne saboda bai samu isashshen lokacin kula da harkokin kasuwancinsa ba

Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa arziƙinsa ya ragu da kaso 12% a shekara huɗun da ya kwashe yana mulkin jihar.

Jaridar The Cable tace da ya ke tattaunawa da ƴan jarida ranar Lahadi, Makinde ya bayyana cewa ya miƙa fom ɗin bayanan kadarorinsa ga ofishin hukumar ɗa'ar ma'aikata (CCB) a birnin Ibadan na jihar.

Gwamna Makinde ya samu karayar arziki
Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

A shekarar 2019, gwamna Makinde yana da dukiya wacce darajarta ta fi N48bn, lokacin da ya bayyana kadarorinsa.

Kara karanta wannan

Zababben Gwamnan Kano, Abba Gida-Gida Ya Bayyana Kadarorinsa Gabanin Rantsar Da Shi

Gwamnan ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba, zai bayyana kadarorinsa a farkon mulkinsa karo na biyu a matsayin gwamnan jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Doka ta yi tanadin cewa sai na bayyana kadarori na bayan wa'adin mulkina na farko sannan kafin na fara mulkina a wa'adi na biyu."
"Ku na sane da kadarorina ko nawa ne a wa'adin mulkina na farko. Ina sanar da ku cewa a shekara huɗun da suka gabata, na talauce da kaso 10% zuwa 12%.

Ya bayyana dalilin karayar arziƙin da ya samu

Gwamnan ya bayyana cewa hakan ya faru ne saboda, bai samu isashshen lokaci ba wajen kula da harkokin kasuwancinsa, cewar rahoton Vanguard.

"Mun mayar da hankali ne wajen kula da harkokin jihar Oyo. Don haka ban yi mamaki ba don an samu asarori nan da can, amma bani da matsala da hakan." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Tara Kwamishinoni da Hadimansa, Ya Tona Asirin Waɗanda Suka Ci Amanarsa

Rantsar da gwamnan a wa'adinsa na karo na biyu zai gudana ne a filin wasan ƙwallon ƙafa na Obafemi Awolowo Stadium, Oke-Ado, Ibadan, a ranar Litinin 29 ga watan Mayun 2023.

Peter Obi Ya Yi Kira Ga 'Yan Najeriya

Rahoto ya zo cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi , ya aike da muhimmin saƙo ga magoya bayansa da sauran ƴan Najeriya, ana dab da rantsar da Tinubu.

Peter Obi ya buƙaci ƴan Najeriya da su zauna lafiya da juna, sannan su kasance masu bin doka da oda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel