Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari Ya Karrama Tinubu, Shettima Da Babbar Lambar Yabo Ta Kasa

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari Ya Karrama Tinubu, Shettima Da Babbar Lambar Yabo Ta Kasa

  • Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya karrama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da lambar yabo ta Grand Commander of the Federal Republic (GCFR)
  • Buhari ya kuma karrama zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da lambar yabo ta Grand Commander of the Order of Niger (GCON)
  • Shugaban ƙasar mai barin gado ya karrama su ne ana saura kwanaki huɗu kafin zuwan ƙarshen wa'adin mulkinsa a ranar 29 ga watan Mayu

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya karrama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da babbar lambar yabo ta ƙasa ta Grand Commander of the Federal Republic (GCFR), a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayun 2023

Shugaban ƙasar mai barin gado ya karrama zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da lambar yabon ne, ana saura kwana huɗu ya bar kujerar shugabancin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bola Tinubu Ya Sanya Labule Da Tsohon Firaministan Burtaniya, Bayanai Sun Fito

Shugaba Buhari ya karrama Tinubu da Shettima
Shugaba Buhari tare da Bola Tinubu Hoto: @Thecable
Asali: Twitter

Shugaba Buhari ya kuma karrama zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da lambar yabo ta ƙasa ta Grand Commander of the Order of Niger (GCON).

Karrama shugabannin masu jiran gado ya wakana ne tare da bayar da rahoton miƙa mulki a ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rantsar da shugaban ƙasar a ranar 29 ga watan Mayu, zai zama karo na bakwai a jere da gwamnatin farar hula ta miƙa mulki ga wata gwamnatin farar hula a tarihin Najeriya.

A ranar Laraba, 1 ga watan Maris 2023, aka bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar wanda aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Har yanzu ana ƙalubalantar nasarar Tinubu a kotu

Tun bayan da aka bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen, jam'iyyun adawa da dama da ƴan takararsu, ciki har da Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party, sun ƙalubalanci nasarar Tinubu a kotu.

Kara karanta wannan

Dan Takarar Sanatan NNPP a Jihar Nasarawa, Ya Sha Da Kyar a Wani Mummunan Hari Da Aka Kai Masa

A farkon wannan watan ne dai, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, ta fara sauraron ƙararrakin da aka shigar akan Bola Tinubu. Kotun za ta ci gaba da zamanta a ranar Juma'a, 26 ga watan Mayun 2023.

Garba Shehu Ya Yi Magana Kan Komawar Shugaba Buhari Jamhuriyar Nijar

A wani rahoton na daban kuma, Garba Shehu mai taimakawa shugaba Buhari kan harkokin watsa labarai, ya bayyana gaskiya kan batun komawar shugaba Buhari, zuwa jamhuriyar Nijar bayan ya bar mulki.

Garba Shehu ya bayyana cewa shugaban ƙasar mai barin gado, raha ce kawai ya ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng