Shehu Sani Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Amurka Ta Turo Wakilai Domin Halartar Rantsar Da Tinubu

Shehu Sani Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Amurka Ta Turo Wakilai Domin Halartar Rantsar Da Tinubu

  • Tsohon sanata, Shehu Sani ya yi bayani kan dalilin da ya sanya shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden, ya turo wakilai domin halartar rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu
  • Sani ya bayyana cewa dalilin gwamnatin Amurka na turo wakilanta zuwa rantsar da Tinubu, yana da nasaba da dangantakar diflomasiyya da kasuwanci
  • A cewar jawabin da ya yi a shafinsa na Twitter, Sani ya bayyana cewa taƙaddamar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba damuwar Amurka ba ce

Abuja - Tsohon sanata wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya bayyana dalilin da ya sanya shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden, ya turo wakilai domin halartar bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Shehu Sani ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ta turo wakilan ne domin halartar rantsar da Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, saboda dangantakar diflomasiyya da kasuwancin da ta ke da ita da Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bola Tinubu Ya Sanya Labule Da Tsohon Firaministan Burtaniya, Bayanai Sun Fito

Shehu ya fadi dalilin Biden na turo wakilai rantsar da Tinubu
Shehu Sani ya yi karin haske kan dalilin Biden na turo wakilai rantsar da Tinubu Hoto: Joe Biden, Shehu Sani, Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

Tsohon sanatan bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter @ShehuSani ranar Talata, 24 ga watan Mayun 2023

Shehu Sani ya ce Amurka ba ta damu da taƙaddamar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba

A cewar tsohon sanatan, gwamnatin Amurka tana kallon taƙaddamar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, a matsayin matsalar Najeriya ce kawai ba ta su ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Ƙasar Amurka tana da dangantakar diflomasiyya da kasuwanci tsakaninta da Najeriya. A dalilin hakan ne ya sanya gwamnatin Amurka ta turo wakilanta domin halartar rantsar da Asiwaju. Abinda Saƙon na su ke nunawa shine taƙaddama kan zaɓen mu, matsalar mu ce ba ta su ba."

Allah Ya Amshi Addu'ar Mu Kan Nasarar Bola Tinubu - Kabiru Gaya

A wani rahoton na daban kuma, sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya, ya yi magana kan nasarar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu ta lashe zaɓen shugaban ƙasa, na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Sanatan ya bayyana cewa Allah ne ya amsa addu'ar da ƴan Najeriya suka yi ta yi domin samun shugabanci nagari, shiyasa Bola Tinubu ya samu nasarar zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel