Gwamna Ortom Ya Bayyana Yarjejeniyar Gwamnonin G-5 Na Raba Kafa Tsakanin Tinubu Da Obi

Gwamna Ortom Ya Bayyana Yarjejeniyar Gwamnonin G-5 Na Raba Kafa Tsakanin Tinubu Da Obi

  • Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya tuna halin da ya shiga a gwagwarmayar ganin shugaban kasa ya fito daga yankin kudu maso gabas
  • Ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi shine zabinsa a zaben
  • Ya bayyana cewa wasu daga cikin takwarorinsa na G-5 sun yi wa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu aiki ne

Gwamna Samuel Ortom ya bayyana cewa ya marawa takarar shugabancin Peter Obi baya gabannin babban zaben 2023.

Ortom ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 24 ga watan Mayu, a shirin kalaci na Arise TV mai suna 'The Morning Show' tare da Reuben Abati.

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue
Gwamna Ortom Ya Bayyana Yarjejeniyar Gwamnonin G-5 Na Raba Kafa Tsakanin Tinubu Da Obi Hoto: Gov Samuel Ortom
Asali: Facebook

Yayin da yake amsa tambayoyi kan shirye-shiryen bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, gwamnan na jihar Benue ya bayyana cewa shi masoyin damokradiyya ne.

Kara karanta wannan

"Na Yafe Maka": Gwamnan Arewa Ya Aike Da Sako Mai Girma Ga Shugaba Buhari

Ya ce soyayyarsa ga damokradiyya ce ta sa ya marawa dan takarar shugaban kasa daga kudu baya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa yayin da takwarorinsa a bangaren G5 na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suka marawa Tinubu baya, shi Peter Obi na Labour Party ne ya kasance zabinsa.

Ortom ya ce:

"Na yi aiki don samun shugaban kasa dan kudu saboda na yarda da adalci, daidaito da gaskiya. Tinubu na daga ciki, Obi na daga ciki. Na zabi yi wa Obi aiki, amma na ce ya kamata shugabancin kasar ya koma wannan wurin (yankin kudu).
"Ina a PDP, a zaben shugaban kasa, na yi wa Obi aiki, sauran takwarorina, hatta a G-5, Tinubu suka yi wa aiki, wanda shine yarjejeniyar da muka yi.
"Zan iya kasancewa PDP sannan na yi aiki don ra'ayin kasar nan don tabbatar da adalci, daidaito da gaskiya."

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Jiga-Jigan Jam'iyyun Adawa Da Tinubu Zai Naɗa Bayan Rantsarwa

Gwamna Ortom ya kuma bayyana cewa alakarsa da PDP da goyon bayansa ga Obi bai hana shi aiki da gwamnati mai zuwa ba, yana mai cewa ya zama dole ra'ayin kasa ya zo kafin ra'ayin kai.

Ya ce:

"Idan gobe aka rantsar da Tinubu, zan ci gaba da yi masa addu'a, zan ci gaba da mara masa baya don ya yi nasara a matsayin shugaban kasar nan.
"Ana ci gaba da shari'a, a bari ta yi aikinta. Yana daga cikin tsarin damokradiyya. Da zaran sakamakon ya fito, duk abun da sakamakon ya kasance, za mu karbe shi kuma duk wanda ya zama shugaban kasa, zan mara masa baya."

Rigima ta kaure tsakanin Femi Gbajabiamila da Wase a Majlisar Tarayya

A wani labarin kuma, mun ji cewa baraka ta shiga tsakanin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da mataimakinsa Idris Wase a ranar Laraba, 24 ga watan Mayu.

Rigimar ta kasance ne a kan halartan taron kaddamar da hedkwatar NILDS wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi a gobe Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng