Dan Majalisar PDP a Jihar Imo Ya Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC
- Ɗan majalisar wakilan jam'iyyar PDP a jihar Imo ya watsawa jam'iyyar ƙasa a ido, inda ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC
- Hon. Jerry Alagbaoso ya bayyana cewa jam'iyyar PDP a jihar Imo ta shiga ruɗani hakan ya sanya ya fice ya bar ta
- Kakakin majalisar wakilan wanda ɗan jam'iyyar APC ne, ya yi murna da komawarsa APC inda ya ba shi wata dama ta musamman
Abuja - Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Orlu/Oru East/Orsu daga jihar Imo a majalisar wakilai, Hon. Jerry Alagbaoso, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.
Jaridar Daily Trust tace ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PDP ne a cikin wata wasiƙa da ya gabatarwa kakakin majalisar Femi Gbajabiamila, a zaman majalisar na ranar Talata.
Ɗan majalisar ya ce ya fice daga jam'iyyar PDP ne saboda ruɗanin da reshen jam'iyyar na jihar Imo ya ke ciki.
PDP Ta Hadu Da Gagarumin Cikas Yayin Da Shugabanni Da Dubban Magoya Bayanta Suka Sauya Sheka Zuwa APC
Alagbaoso ya bayyana cewa komawarsa jam'iyyar APC, zai ba shi dama ya yi aiki tare da gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, domin ciyar da jihar gaba, cewar rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Abubuwa sun rincaɓe a jam'iyyar PDP ta jihar Imo. Hakan ya bayyana dalilin da ya sanya ƴan majalisa guda uku daga jihar Imo suka fice zuwa jam'iyyar APC, ƴan makonnin da suka wuce."
"Ni ma ba za a bar ni a baya ba, duba da ruɗanin da jam'iyyar PDP a jihar Imo ta samu kanta a ciki."
Gbajabiamila ya yi farin ciki da komawarsa jam'iyyar APC
Gbajabiamila ya bayyana komawar Alagbaoso jam'iyyar APC, a matsayin wata gagarumar guguwar siyasa duba da matsayin da ya ke da shi a siyasance.
Ya ce hakan ya sanya ya bar shi ya karanta wasiƙar ficewarsa daga PDP da kansa, maimakon yadda aka saba inda kakakin majalisa ne ya ke karanta wasiƙar da ƴan majalisa masu sauya sheƙa suka kawo.
Kotu Ta Tsige Ɗan Majalisar Dokoki Kan Ya Sauya Sheka Zuwa PDP
A wani labarin na daban kuma, kotu ta tsige ɗan majalisar dokoki saboda ya fice daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP a jihar Bauchi.
Hon. Musa Baroro ya yi asarar kujerarsa ne bayan ya tsallaka zuwa jam'iyyar PDP a shekarar da ta wuce.
Asali: Legit.ng