Zaben 2023: Kotun Koli Ta Tsaida Ranar Sauraron Shari’ar PDP v Tinubu da Shettima
- Babban kotun kasar nan ta tsaida ranar da za ayi hukunci a karar da jam’iyyar PDP ta shigar
- Lauyoyin PDP sun roki kotu ta ruguza takarar Bola Tinubu da Kashim Shettima a karkashin APC
- A ranar Juma’a Alkalan kotun koli za su zartar da hukuncin da zai kasance na karshe a shari’ar
Abuja - Kotun koli ta daga sauraron shari’a zuwa ranar 26 ga watan Mayu 2023 domin cigaba da yanke hukunci a karar da jam’iyyar PDP ta kai.
Rahoton ya fito yanzu nan daga jaridar Vanguard bayan zaman kotun da aka yi a ranar Litinin.
Babbar jam’iyyar hamayyar kasar ta na rokon kotun koli ta ruguza takarar da Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima su ka yi a karkashin APC.
Jam’iyyar PDP ta na so kotun Allah ya isa ta yi watsi da hukuncin Mai shari’a James Abundaga wanda ya soke karar da Lauyoyinta suka shigar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkali James Abundaga na kotun daukaka kara ya ce PDP ba ta iya gamsar da shi har ya soke takarar ‘ya ‘yan na jam’iyyar APC mai mulki ba.
Kamar yadda Punch ta tabbatar, sai nan da kwanaki hudu Bola Tinubu da abokin gaminsa a zaben bana, Shettima za su san makomarsu.
Hukuncin zai zo ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen mika mulki ga sabon shugaban kasa. A mako mai zuwa ne za a canza gwamnati.
Daily Trust ta ce Mike Ozekhome (SAN) ne Lauyan da ya shigar da kara a madadin PDP, ya ce Shettima ya shiga takara biyu a zaben da aka yi.
Lauyan ya na ikirarin zababben mataimakin shugaban kasar ya fara shiga takarar Sanata kafin Bola Tinubu ya zama abokin gaminsa a 2023.
Zaben Jihar Ogun
A rahoton da muka fitar a baya, an ji Ladi Olatunde Adebutu ya samu kan shi cikin matsala domin 'yan sanda su na bincike a kan shi kan sayen kuri’u.
Duk da N2bn da ake zargin Adebutu ya kashe, Jam’iyyar APC ta doke shi da ratar kuri’u 13, 915. Yanzu haka ya bar kasa da sunan ana neman kashe shi.
Asali: Legit.ng