Fusatattun ‘Yan Takaran Majalisa 7 Sun Fadi Yadda Za Su Karya Bola Tinubu da APC

Fusatattun ‘Yan Takaran Majalisa 7 Sun Fadi Yadda Za Su Karya Bola Tinubu da APC

  • ‘Yan kungiyar G7 da suka kafa COPSA a Majalisa, ba za su goyi bayan Hon. Tajudeen Abbas ba
  • Bayan wani taro da su ka yi a Abuja, Hon. Yusuf Gagdi ya sanar da matsayar da suka hadu a kai
  • Masu takarar shugabancin majalisa sun zauna da ‘yan adawa a karkashin jagorancin Fred Agbedi

Abuja - Wasu masu neman shugabancin majalisar tarayya sun amince su hada-kai domin kalubalantar Tajudeen Abbas da jam’iyyar APC ta tsaida.

Rahoton Premium Times ya ce ‘yan kungiyar COPSA da aka fi sani da G7, za su zabi mutum guda a cikinsu da zai gwabza da ‘dan takaran APC mai ci.

‘Yan kungiyar COPSA majalisa sun hada da Ahmed Idris Wase, Muktar Aliyu Betara, Sada Soli, Aminu Jaji, Yusuf Gagdi da kuma Hon. Miriam Onuoha.

Kara karanta wannan

‘Dan Majalisar APC Ya Tona Dalilin da Ya Sa Gbajabiamila Yake So Abbas Ya Gaje Shi

‘Yan Takaran Majalisa
Hon. Ahmad Wase a Majalisa Hoto: @femigbaja
Asali: Twitter

Wadannan ‘yan majalisa da duka ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ne za su yi wa Hon. Tajudeen Abbas taron-dangi, su hana shi kai labari a zaben bana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A yayin da ‘yan COPSA suka yi wani zama a ranar Lahadi a wani otel da ‘yan jam’iyyar adawa a majalisa ne suka fadi matsayar da suke shirin dauka.

‘Dan majalisar Bayelsa a karkashin PDP¸ Fred Agbedi ya jagoranci ‘yan adawa su ka hadu da G7.

Jawabin Soli bayan haduwa da Agbedi

Rahoton ya ce ‘Yan siyasar sun kyakyansa shirin na su a wannan zama a lokacin da Sada Soli mai wakiltar mazabar Jibia a Katsina ya yi jawabi da bakinsu.

Hon. Sada Soli ya fadawa Duniya cewa ba da dadewa ba za su sanar da ‘dan takaransu, kuma ya ce dukkkaninsu za su goyi bayan wanda aka tsaida.

Kara karanta wannan

‘Yan PDP, LP da NNPP Fiye da 100 Su Na Goyon Bayan ‘Dan Takaran APC a Majalisa

‘Dan majalisar ya ce ba za su goyi bayan ayi masu karfa-karfa ba, a tsaida masu shugabannin da ba su so a majalisar wakilan tarayya a mako mai zuwa.

Tsintsiya madaurinki daya

Tribune ta ce Hon. Yusuf Gagdi ya ce dukkansu sun yarda za su fito da ‘yan takara guda da za su nemi kujerar shugaban majalisa da kumaa mataimakinsa.

A jawabin da ya fitar, Gagdi ya jaddada matsayar da takwaransa suke kai na fito da shugaban majalisa, ya ce amma sai nan gaba za su ayyana ‘dan takarar.

Buhari da Yemi Osinbajo za su sauka

Ku na da labari Gwamnatin da za ta gaji shugabancin Najeriya a makon gobe ta na da aiki a gabanta yayin da Bola Tinubu da Kashim Shettima za su shiga ofis.

Akwai bashin N77tr da manya-manyan ayyukan da gwamnati mai barin gado ba ta iya karasawa ba. Tinubu zai fara cin karo da su a fadar Aso Rock Villa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng